Ziyarar Erdogan Algeriya cikin hotunan Afirka

An wallafa

Ƙayatattun hotunan Afirka da na 'yan nahiyar a wasu sassan duniya

.

Asalin hoton, Jalal Morchidi/EPA

Bayanan hoto, Tawagar makaɗa daga ƙasara Colombia kenan ke rawa a lokacin bikin baje-kolin waƙoƙi karo na 10 da aka gudanar a birnin Rabat na ƙasar Morocco ranar Laraba.
h

Asalin hoton, Aaron Ufumeli/EPA

Bayanan hoto, Wani mai sayar da abaeba kenan a gefen titin birnin Harare na ƙasar Zimbabwe, yayin da ƙasar ke tsaka da fuskantar ɓarkewar cutar kwalara.
d

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, shugaban Turkiyya Racep Tayyip Erdogan kenan yayin da ake yi masa faretin girmamawa ranar Talata lokacin wata ziyara da ya kai birnin Algiers na ƙasar Algeriya
.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Yadda mazauna gundumar Kisauni a birnin Mombasa na ƙasar Kenya suka fuskanci mummunar ambaliya ruwa ranar Juma'a
.

Asalin hoton, epa

Bayanan hoto, Magoya bayan shugaban ƙasar DR Congo President Felix Tshisekedi ke rawa a filin wasa na Martyrs da ke birnin Kinshasa ranar lahadi, a lokacin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓensa
.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ranar Alhamis kenan, lokacin da Falasdinawa masu bizar ƙasashen waje suka isa kan iyakan Rafah ta ƙasar Masar, yayin da rikici tsakanin Isra'ila da Hamas ke ci gaba a Gaza.
d

Asalin hoton, VATICAN MEDIA HANDOUT

Bayanan hoto, Fafaroma Francis ke gaisawa da Mbengue Nyimbilo Crepin, wani ɗan ci-rani daga Kamaru, a lokacin da suka haɗu da tawagar masu ceto ta tekun Bahar Rum, a fadar Vatican.