Harry Kane ya ci kwallo biyu a wasan Bayern Munich

An wallafa

Kyaftin din Ingila Harry Kane ya zura kwallo biyu a wasansa na farko a gida a Bundesliga a filin wasan Allianz, bayan da zakarun gasar bara suka doke Augsburg.

Kane ya zama dan wasan Ingila na farko da ya zura kwallo a wasa biyu na farko a Bundesliga, wanda ya ci fenariti dab da za a tafi hutun rabin lokaci.

Tsohon dan wasan gaban Tottenham ya ci kwallonsa na biyu bayan an dawo hutun rabin lokaci inda Bayern ta lashe wasan da ci 3-1.

Bayern tana da maki shida, kamar Union Berlin da Bayer Leverkusen da Wolfsburg da kuma Freiburg.

A wasanta na gaba Bayern za ta fafata da Borussia Munchengladbach a ranar 2 ga watan Satumba.