Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dan shekara 13 da ya zana gadar sama da gwamnan Borno ya bai wa kyautar N5m
“Lokacin da na haife shi, burina a kansa shi ne, na ganin ya zama malamin makaranta, sai dai a lokacin da ya cika shekara uku, na lura cewa idan yana wasa da ƙasa ko taɓo a waje, da ƙyar nake tursasa shi ya dawo cikin gida.’’
Malama Hafsa Musa, ita ce mahaifiyar yaron nan ɗan shekara 13 da aka dinga magana a kansa a arewa maso gabashin Najeriya a baya-bayan nan, mai suna Musa Sani.
A kwanakin baya ne gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya bai wa mahaifan Musa kyautar kuɗi har naira miliyan biyar domin sanya yaron a makaranta.
Ya yi hakan ne bayan da bidiyon yaron na yadda ya kwaikwayi gina gadar sama ta Maiduguri suka karaɗe shafukan sada zumunta a arewacin Najeriya.
A cewar gwamnan, Musa ya nuna cewa yana da fikira, kuma shi yasa gwamnati ta bai wa mahaifansa kyautar kuɗin domin saka shi a makaranta saboda burinsa ya cika.
Kamar sauran iyalai da dama a arewacin Najeriya, mahaifan Musa na da yara da yawa, kuma Musa ya kasance ɗa na huɗu da Mallam Sani ya haifa cikin yaransa 10.
Mahaifiyarsa ta ce ba za ta iya tuna sau nawa ya kwanta rashin lafiya ba saboda yawan wasa cikin ƙasa da kuma taɓo da yake yi.
"Tun yana ƙarami, ya kan zauna ya riƙa gina gidaje da sauran abubuwa daban-daban da taɓo, a yawancin lokuta, ya kan kamu da sanyi saboda jikinsa na cikin sanyi a ko da yaushe.’’
"Daga wancan lokaci, ina ji a jikina cewa yarona yana da fikira a ɓangaren harkokin injiniya, wanda hakan ne ya sa na manta da burina na farko da na yi a kansa na zama malamin makaranta.’’
''Na sanya shi wargaza gadar sama da ya gina da farko, amma sai ya sake gina ta"
"Ita gadar sama da ya gina da farko, na umurci ya wargaza ta saboda mutane da ke zuwa kallonta sun jawo cunkoson da ya kai har wasu suka ji raunuka."
Mahaifiyar ta ce daga baya, yaron sai ya sake gina ta baya aiko ɗan sako da Gwamna Babagana Zulum ya yi zuwa gidansu.
Malama Hafsat ta kuma ce tana alfahari da ɗanta bayan karrama su da Gwamna Zulum ya yi kuma abu ne da ba za ta manta ba tsawon rayuwarta.
Ta shawarci iyaye da su riƙa barin ƴaƴansu su yi abin da suka fi so, wataƙila hakan zai fito da fikira da fasaharsu.
"A yanzu, akwai yayyensa mata biyu da wani yayansa da su ma suke zane-zane, amma shi ne Allah ya ɗaukaka kawo yanzu."
A nasa ɓangare, Musa mai shekara 13 da yanzu yake aji hudu a makarantar firamare, ya ce aikin zane-zane na ɓangaren injiniya shi ne abin da yake fatan yi tsawon rayuwarsa.
Ya kuma ce a yanzu ya zama abin alfahari a cikin ajinsu, inda dukkan ɗalibai ke zuwa ɗaukar hoto tare da shi.
"Ina alfahari da kaina da kuma gadar sama da na yi, ina kuma fatan gina wacce tafi ta watarana."
Musa ya ce a yanzu zai mayar da dukkan hankali kan karatunsa saboda shi ne abin da zai taimaka masa cimma dukkan burinsa a rayuwa.
Yadda gwamnatin Borno ta gano fikirar Musa
El Lawal Mustapha shi ne mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Borno, ya faɗa wa BBC Pidgin cewa gwamnan jihar ya sami ganin gadar saman da yaron ya gina ne lokacin da bidiyonsa ya karaɗe intanet.
"Bayan gwamnan ya sami kallon bidiyon a wayarsa, sai ya ce min na je na binciko inda yaron da kuma mahaifansa ke zaune.
"Daga nan sai na fara nema, lokacin da na gano gidansu yaron sai aka yi rashin sa’a, inda mahaifiyarsa ta ce baya nan saboda mutane da yawa da ke zuwa suna matsa musu."
"Kafin na fada mata cewa Gwamna Zulum ne ya aiko ni."
Jami’in ya ce yana fatan wannan labari na Musa zai ƙara wa matasa da yawa ƙaimi ba a Borno kaɗai ba, a duk fadin Afirka wajen fito da irin basirar da Allah ya ba su.