Naby Keita ba zai buga wa Werder Bremen wasa biyu ba

An wallafa

Werder Bremen za ta buga wasa biyu ba tare da sabon ɗan kwallon da ta ɗauka a bana ba Naby Keita, sakamakon raunin da ya ji.

Ƙungiyar da ke buga gasar Bundesliga ce ta sanar da hakan ranar Lahadi.

Tsohon ɗan wasan Liverpool mai fama da jinya ya buga wasa ɗaya ranar Asabar da Hoffenheim ta doke su 3-2 a lik.

Bremen ta sanar da cewa ɗan kwallon ya ji rauni a wasan na ranar Asabar, inda ta sauya shi bayan da suka shiga zagaye na biyu a fafatawar.

''Abin takaici ne ga Keita, bayan da ya gama jinya ya fara yi mana tamaula sai ga shi zai ci gaba da wata jinyar.

''Amma dai ba zai buga mana wasa biyu da za mu buga nan gaba ba, bayan fafatawar ƙasa da ƙasa,'' in ji Clemens Fritz, shugaba da ke kula da tamaular ƙungiyar.

Kenan Keita ba zai yi wasa ba ranar 20 ga watan Oktoba a gidan Borussia Dortmund da kuma wanda za su karɓi bakuncin Union Berlin mako ɗaya tsakani.