Mutumin da ya kwashe shekara 62 yana sauraron rediyo
Mutumin da ya kwashe shekara 62 yana sauraron rediyo
An wallafa
Yayin da ake tunawa da ranar sauraron rediyo ta duniya a 13 ga watan Fabarairun kowace shekara, BBC ta tatauna da Mallam Abdullahi Harisu wanda ya kwashe shekara 62 yana sauraron rediyo.
Ya ce sauraron rediyo ya sanya al'ummar unguwarsu na gaskata duk wani abu da ya faɗi kasancewar ana masa kallo wanda ke da masaniya kan abubuwan da ke faruwa a faɗin duniya.



