Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mbappe zai maye gurbin Ronaldo a Man Utd, Kungiyoyin Premier na rububin Skriniar
Manchester United na shirin maye gurbin Cristiano Ronaldo, da Kylian Mbappe.
Kociyan United Erik ten Hag ya ce Ronaldo ba zai sake buga wa Manchester United wasa ba bayan wata hira ta zazzage-zuciyarka da dan wasan na Portugal ya yi da dan jarida Piers Morgan.
Dan bayan da Manchester United ke harin saye Benjamin Pavard, ya ce a shirye yake ya tafi AC Milan daga Bayern Munich duk da alakanta dan Faransar mai shekara 26 da ake yi da Red Devils din.
Manchester City da Chelsea da Tottenham da Liverpool da Arsenal da kuma Manchester United, dukkansu na sha’awar sayen dan bayan Slovakia Milan Skriniar, inda Inter Milan ke fatan zai sabunta yarjejeniyarsa da ita.
Shugaban Barcelona Joan Laporta ya ce kungiyar ba za ta iya sayen wani sabon dan wasa ba a watan Janairu sai dai idan an sauya tsarin gasar kasar ta La Liga.
Watakila Manchester City ta yi zawarcin dan wasan tsakiya na Jamus Tony Kroos, amma kuma Real Madrid na fatan zai sabunta kwantiraginsa da ita.
Leicester da Everton da Brighton na sha’awar sayen mai tsaron ragar Lens da Faransa Brice Samba, mai shekara 28.
Matashin dan wasan tsakiya na Liverpool, Fabio Carvalho, da a da yake tawagar matasa ta Ingila ya sanar da ficewa daga tawagar ‘yan kasa da shekara 21 ta Portugal ta hanyar aikawa da sakon kar-takwana na waya.
West Ham ta gaya wa kociyanta David Moyes cewa kada ya yi wata fargaba dangane da aikinsa a yanzu bayan da kungiyar ta yi rashin nasara karo na tara a wannan kakar ranar Asabar.
Brighton na sha’awar sayen babban dan bayan Shakhtar Donetsk da Ukraine Mykola Matviyenko mai shekara 26.