Ramukan da ke haifar da haɗurran motoci a Abuja

Bayanan bidiyo, Yadda ake cire murafun magudanun ruwa a Abuja
Ramukan da ke haifar da haɗurran motoci a Abuja
An wallafa

Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, na daya daga cikin manyan biranen Afrika da ke tutiya da ababan more rayuwa irinsu manyan tituna da sauransu.

Sai dai wani kalubale da ke jawo koma-baya ga cin gajiyar wadannan tituna, shi ne yadda ake cire murafun ramukan magudanun ruwan da ke karkashin titunan.