Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ba a tsare mai goyon bayan Ingila ko Wales ba a Qatar
Ba a tsare mai goyon bayan Ingila ko Wales ba a Gasar Cin Kofin Duniya a lokacin da suka kara a fafatawar rukuni a Qatar.
Burtaniya ta tura 'Yan sanda zuwa Qatar, domin suke shiga tsakani da tsawatarwa a lokacin da tawagogin ke buga wasanninsu kada a samu matsala.
Babban jam'in 'Yan sanda mai kula da tsaro a fannin tamaula, Mark Roberts ya yaba wa magoya baya kan yadda suka bi doka a Qatar da nuna halaye na gari.
Sai dai an tsare mutane 531 da suka shafi tayar da yamutsin da ya shafi tamaula a Burtaniya.
150 daga ciki sun faru ne a daren ranar Asabar lokacin da Ingila ta yi rashin nasara a hannun Faransa a Qatar da ci 2-1 a Quarter finals.
Jumulla an tsare mutum 115 a Burtaniya tun bayan da aka fara gudanar da Gasar Cin Kofin Duniya, inda aka samu yamutsin a wajen kallon tamaula.
A irin wannan lokacin a Gasar Kofin Duniya a Rasha a 2018, an tsare mutum 225 a Burtaniya kan tayar da yamutsin da ya shafi kallon tamaula.
Roberts ya ce hana shan barasa da mahukuntan Qatar da suka yi ya taimaka da magoya baya suka nuna hali na gari.
Ingila ta doke Wales 3-0 a karawar rukuni na biyu a Gasar Kofin Duniya ranar 29 ga watan Nuwamba, inda ta ja ragamar rukunin da maki bakwai.