Kalubale shida ga yunkurin takarar Trump a wannan karon

Asalin hoton, Getty Images
Donald Trump ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban Amurka karo na uku a jere, a wani yanayi na ba kasafai ba a yunkurin da tsohon shugaban kasar yake yi na sake komawa fadar White House bayan ya sha kaye a zaben 2020.
A jawabin da ya yi na fiye da awa daya lokacin kaddamar da takarar tasa, ya rika cika baki game da ayyukan da ya yi yayin da yake shugaban kasar sannan ya soki shekaru biyu na mulkin Joe Biden.
Jawabin nasa ya fito da wasu daga cikin manyan abubuwan da Mr Trump ya yi fice a kansu. Yana da basira sosai wajen sanin batutuwan da suka fi jan hankalin mutanensa masu tsattsauran ra'ayi, irin su ci-rani da laifuka.
Yana da miliyoyin magoya baya 'yan ga-ni-kashe-ni. Bayan ya kwashe shekara hudu a kan mulki, yawancin masu goyon bayansa suna rike da manyan mukamai a jami'yyarsu ta Republican.
Sai dai jawabin nasa ya kuma fito da wasu daga cikin gazawar Mr Trump.
Ya boye wahalar da Amurkawa suka sha sakamakon kura-kuran da ya yi lokacin barkewar annobar korona kuma bai ce komai ba game da watannin da shi da magoya bayansa suka kwashe suna ikirarin cewa bai sha kaye a zaben shugaban kasa na ranar 6 ga watan Janairu 2020 ba lamarin da ya sa magoya bayan nasa suka kai hari a Majalisar Dokokin kasar.
Ya yi yunkurin kare rashin katabus din jam'iyyarsu ta Republican a zaben rabin wa'adin mulkin da aka gudanar a makon jiya da kuma shan kayen da 'yan takarar da ya mara wa baya suka yi, lamarin da ya jawo masa suka daga wurin masu ra'ayin rikau.
Mr Trump ya ce aikin da ke gabansu b a na "gama-garin dan takara" ne, yana mai cewa na miliyoyin mutane ne - magoya bayansa da masu yi masa yakin neman zabe. Ya jagoranci wadannan mutane wajen samun nasara a zaben da aka yi masa shekaru shida da suka gabata, sai dai akwai dalilai da ke nuna cewa zai gamu da kalubale a wannan karon a yunkurinsa na sake komawa fadar shugaban kasar. Ga wasu daga cikinsu:
1. Abubuwan da ya yi a baya
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Shekaru takwas da suka gabata, Mr Trump sabon-shiga ne a harkar siyasa. Bai rike wani mukami da za a auna ayyukan da ya yi ba, don haka a wancan lokacin masu kada kuri'a suna fatan zai cire musu kitse daga wuta. Ya yi alkawura da dama, ba tare da wani ya soke shi kan abin da ya yi ko bai yi ba a baya.
Wannan karon ba haka batun yake ba. A yayin da za a iya cewa Mr Trump ya samu nasarori da dama a shekaru hudu da ya kwashe a kan mulki, ciki har da rage haraji da kuma gyaran fuska a kan dokar aikata manyan laifuka, a gefe guda kuma a iya cewa ya tafka wasu kura-kurai.
'Yan jam'iyyar Republican ba za su manta da gazawarsa wajen soke gyaran fuskar da jam'iyyar Democrat ta yi a game da inshorar lafiya ba da kuma alkawuran da ya rika nanatawa cewa zai zuba jari a harkokin ababen more rayuwa wadanda bai cika ba. Sai kuma gazawar Mr Trump wajen shawo kan annobar korona, batun da zai jawo masa suka daga bangarori daban-daban.
Tuni dai 'yan jam'iyyar Democrat suke sukarsa bisa rashin daukar matakin da ya dace a lokacin barkewar annobar.
2. Harin da aka kai a Majalisar Dokokin Amurka ranar 6 ga watan Janairu
Baya ga sukar da Mr Trump zai sha kan kare nasarorinsaa yayin da yake shugaban kasa, zai kuma kare kansa game da rawar da ya taka lokacin da yake dab da sauka daga kan mulki da kuma wacce ya taka a mamayar da wasu magoya bayansa suka yi wa Majalisar Dokokin kasar ranar 6 ga watan Janairun 2021.
Hotunan da aka dauka a ranar, wadanda suka nuna magoya bayan Trump rike da alluna da kyallayen da ke dauke da hotunansa, a yayin da ake fesa musu barkonon-tsohuwa, sun mamaye majalisar dokokin inda suka yi yunkurin hana mika mulki, ba za a taba mantawa da su ba.
Zaben rabin wa'adin mulkin da aka gudanar a makon jiya ya nuna cewa abin da ya faru a ranar - da kuma kalamai da halin-ko-in-kula da Mr Trump ya nuna kafin mamayar majalaisar dokokin - ya nuna cewa batun zai iya yin tasiri a zukatan masu kada kuri'a.
'Yan takarar jam'iyyar Republican da dama da suka goyi bayan Mr Trump lokacin da ya ki amincewa da shan kaye a zaben 2020 sun fadi a zaben rabin wa'adin zango. Da dama daga cikinsu sun sha kayea hannun wasu 'yan Republican a jihohinsu wadanda ba su goyi bayan Trump ba.
3. Zai fuskanci shari'a
Daya daga cikin dalilan da ake gani sun sa Mr Trump yake zumudin sake kaddamar da takarar shugaban kasa shi ne domin ya samu damar jan hankalin masu zabe cewa ana gudanar da jerin binciken a kansa ne domin cimma wata manufa ta siyasa.
Ko da yake mutane za su iya amincewa da kalamansa kan batun, amma a fili yake cewa laifukan da ake zargin Mr Trump da aikata a zahiri suke.
A halin da ake ciki tsohon shugaban kasar na Amurka yana kare kansa game da zargin tsoma baki wajen karkata sakamakon zabe a Georgia, da kuma zargin cewa ya sanya baki a wani yunkuri na zamba cikin aminci a harkokin kasuwancinsa a New York, da kuma zargin bata suna a wata shari'a da ta shafi cin zarafi, da kuma wani bincike da gwamnatin tarayya take yi masa kan rawar da ya taka a mamayar da magoya bayansa suka yi wa majalisar dokokin kasar da kuma yadda ya boye wasu bayanan sirri bayan saukarsa daga kujerar shugaban kasa.
Kowanne daga cikin wadannan zarge-zarge zai iya sa wa a tuhumi Mr Trump lamarin da ka iya yin kafar-ungulu ga yakin neman zabensa.
Ko babu komai, za su janye hankalinsa daga yakin neman zaben. Ko kuma su sa a ci tararsa ko ma ya tsinci kansa a kurkuku.
4. Babban abokin hamayya
A yayin da aka soma yakin neman zaben fitar da gwani na dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Republican shekaru takwas da suka gabata, Mr Trump ya fafata da gwamnan Florida wanda ake ganin ba zai yi nasara ba. An yi tsammanin shi ma Jeb Bush zai taka rawar gani, ko da yake daga karshe bai yi katabus ba.
Duk da sunan da ya yi da kuma kallonsa a matsayin wanda zai iya bugar kirji amma bai kai labari ba.
Ra'ayinsa ya sha bamban da na yawancin 'yan Republican a kan ci-rani da tsare-tsare kan ilimi.
Sannan sunan Bush bai yi tasiri ba kamar yadda ya yi a baya.

Asalin hoton, Getty Images
Idan Mr Trump yana so ya sake tsayawa takara a zaben 2024, watakila sai ya sake fafatawa da gwamnan Florida.
Sai dai ba kamar Mr Bush ba, Ron DeSantis ya sake lashe zaben gwamnan jiharsa da gagarumin rinjaye lamarin da ke nuna cewa yana yana da goyon bayan 'yan jam'iyyar. Ko da yake har yanzu ba a taba gwada farin jininsa a kasa baki daya ba, amma tauraruwarsa tana haskakawa yanzu haka.
Kawo yanzu babu tabbas ko Mr DeSantis zai tsaya takarar shugaban kasa a jam'iyyar Republican.
Gwamnan na Jihar Florida zai iya zama dan takarar da 'yan jam'iyyar wadanda ba sa so Mr Trump ya sake samun dama. Idan haka, masu kada kuri'a na jam'iyyar Republican tana da zabin hana Mr Trump tsayawa takara.
5. Rashin farin jini
Kwanaki kadan kafin Mr Trump ya kaddamar da takararsa ta shugaban kasa, wata kungiyar masu ra'ayin rikau ta fitar da jerin sakamakon kuri'a kan ra'ayin jama'a da ke nuna Mr Trump yana bayan Ron DeSantisa cikin masu iya yi wa Republican takara a jihohin Iowa da New Hampshire.

Asalin hoton, Getty Images
Wadannan jihohi su ne suke soma kada kuri'a a zaben fitar da gwani na dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Republican.
Kazalika Mr DeSantis ya sha gaban Mr Trump da maki 26 a Florida da kuma maki 20 a Georgia, inda za a sake gudanar da zaben Sanata a watan Disamba.
Bincike ya nuna cewa goyon bayan Mr Trump yana ci gaba da raguwa a dukkan wadannan jihohi.
Kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta baya bayan nan a game da zaben rabin wa'adin mulkin da aka kammala makon jiya ta nuna cewa Mr Trump ba shi da farin jini - ciki har da a manyan jihohi da yake bukata kafin ya samu damar lashe zaben shugaban kasa.
A jihar New Hampshire, kashi 30 na masu kada kuri'a ne kawai suka ce suna so Mr Trump ya sake tsayawa takarar shugaban kasa. Ko a can Florida masu goyon bayansa ba su zarta kashi 33 ba.
6. Shekarunsa sun ja
Idan Mr Trump ya sake yin nasara a zaben shugaban kasa, zai kasance mai shekara 78 yayin da zai sha rantsuwar kama aiki. Ko da yake a lokacin shekarunsa za su yi daidai da na Joe Biden lokacin da ya shiga fadar White House, zai zama shugaban kasa na biyu mafi shekaru a tarihin Amurka.
Yawan shekaru suna yin tasiri sosai ta hanyoyi daban-daban ga shugabanni, kuma yawan aikin da ke kan shugaban kasar ma haka.
Babu wani tabbaci cewa Mr Trump zai iya jure wa wahalhalun da ke tattare da yakin neman zaben fitar da gwani na jam'iyyar Republican - musamman inda zai fafata da matasan 'yan takara.
A baya Mr Trump ya nuna karsashi sosai, sai dai ko wanne mutum yana da iyakarsa.











