Abin da 'yan Najeriya ke cewa game da kasafin kuɗin Buhari na ƙarshe

An wallafa

'Yan Najeriya ciki har da shafukan sada zumunta na ci gaba da tsokaci a kan ƙudurin kasafin kuɗin 2023 da Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar na kimanin naira tirliyan 20.

Kasafin kuɗin na shekara mai zuwa, an gabatar da shi ne ranar Juma'a a wani zaman haɗin gwiwar majalisar dattijai da ta wakilai kuma ana sa ran cewa sai gwamnati ta ciyo bashi na fiye da rabin kasafin kuɗin don cike giɓi.

Muhammadu Buhari ya ce an tsara ƙudurin kasafin kuɗin 2023 ne ta yadda zai yi ingantacciyar shimfiɗa da share hanya ga gwamnatin da za ta gaje shi.

An tsara kasafin kuɗin ne don ya tunkari wasu manyan matsaloli da ke addabar ƙasar tare da kafa harsashi ga gwamnatin da ke tafe.

Za dai a samo kuɗaɗen aiwatar da kasafin kuɗin ne ta hanyar sayar da wasu kadarorin gwamnati in ji shugaba Buhari, baya ga basukan da za ta ciwo.

Babban abin damuwa

Sanata Kabiru Ibrahim Gaya, ɗan majalisar dattijai daga Kano ya ce babban abin damuwa game da kasafin kuɗin shi ne babu sa ran samun kuɗi daga kamfanin samar da man fetur na ƙasa.

A cewarsa, kuɗin da kamfanin ya samu yana zurarewa ne wajen biyan tallafin man fetur da sauran harkoki.

"Saboda haka dole aka sa sai an ciyo bashi, mai ɗumbin yawa, kusan rabin abin da za a kashe a ƙasar na bashi ne.

To amma, in dai ana so ƙasa ta rayu dole sai an bi ta haka. Ran da aka samu buɗi (abu) ya yi kyau, sai a biya bashin a ɗora".

Sanata Kabiru Gaya ya ce kasafin kuɗin yana sa ran ciyo bashin kuɗi kimanin naira tirliyan 11 don cike giɓinsa.

Shi ma shugaban kwamitin kasafin kuɗi na majalisar dattijai, Sanata Barau Jibrin ya ce ko da yake ba za su yi gaggawar yin tsokaci a kan ƙudurin kasafin ba har sai an tantance abin da kasafin ya ƙunsa.

Duk da haka ya ce: "Babban abu dai shi ne, kuɗin da za a yi aikace-aikacen gina ƙasa (manyan ayyuka) a wannan karon ya ragu. Ba kamar na bara ba. Bara an samu kuɗi kimanin tirliyan 2.7 sai dai a wannan karo kuɗin ba zai fi naira tirliyan 1 da 'yan kai ba".  

Kundin bashi

Tun bayan gabatar da ƙudurin kasafin 2023, 'yan Najeriya ke ta bayyana ra'ayoyi kan abin da kasafin kuɗin na shekara mai zuwa ya ƙunsa daga ciki akwai ra'ayin Mansur Babawuro Nafada wanda ya ce "To muna fatan Allah ya sa talakawan Najeriya za su ga tasirin kasafin kuɗin 2023 da Shugaba Buhari ya gabatar..... domin fa an daɗe ana ruwa ƙasa tana shanyewa".

Shi kuwa Habeeb Idriss cewa ƙudurin kasafin kuɗin 2023, ba komai ba ne face wani kundin bashi da za a ciyo wa al'ummar ƙasar.

Shi ma Usaini Sidi ƙorafi yake yi kan batun gabatar da kasafin kuɗin, inda ya ce: "Allah sarki talakan Najeriya! Allah ya ba mu shugabanni nagari ko talaka ya san ana yi da shi. Duk kasafin kuɗin da ake yi, mu har yanzu ba mu gani a ƙasa ba, tsadar rayuwa ta yi yawa.

Yayin da Zakariya'u Imam Zaks ke fatan cewa "Allah ya sa (ƙudurin kasafin kuɗin 2023) ya zama mai amfani ga al'ummar ƙasar nan".

Sai Halad Garba da ke cewa: "Allah ya sa a cirewa ƙungiyar malaman jami'o'i ta ƙasa (ASUU) kasafinsu (don) mu ma, mu koma karatu".

Yayin da Aminu Adamu Malam Madori ya ce "To muna fatan wannan kasafin kuɗi ya taimaka wajen inganta rayuwar al'ummar ƙasarmu Najeriya".

Muhammad Adam Haruna kuwa ya ce "Da tambayata za ta je inda ya dace da sai na ce shi kuma kasafin (kuɗin) shekarar da muke ciki ina aka yi da shi?"

Masana tattalin arziƙi dai na gargaɗi ga gwamnatin Najeriyar, ganin cewa mafi yawan kasafin kuɗinta yana ƙarewa ne wajen biyan bashi maimakon gudanar da ayyukan inganta ilmi da kula da lafiya.

Ko da yake, shugaban ƙasar ya ce gwamnatinsa ba ta da zaɓi illa ta karɓi rance don fitar da ƙasar daga ƙangin da ta shiga na komaɗar tattalin arziƙi har sau biyu a cikin shekara bakwai.