Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda kulle mashigar Rafah ke neman mayar da Falasɗinawa nakasassu
- Marubuci, Mahmoud Elnaggar and Waleed Hassan
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- An wallafa
Gwamnatin yankin Falasɗinawa da ke riƙe da akalar hanyoyin shiga Gaza ta ruwaito cewa tun watan Mayu hanyoyin shiga Rafah da Kerem Shalom suke a rufe. BBC ta tattauna da wasu ƴan Gaza da ke buƙatar kulawar likitoci a wajen zirin Gaza, dangane da yadda rufe mashigar guda biyu ta shafe su.
"Mun kwashe watanni muna jiran ranar da zai tafi Misra," in ji 'yar Falasɗinu idanunta cike da hawaye a lokacin da ta zauna kusa da gadon da ɗanta yake kai a asibiti.
Lubna Salem mahaifiya ce ga Amin - yaro mai shekaru uku wanda harin Isra'ila a tsakiyar Gaza a watan Disambar bara ya raunata.
Ya kamata Amin ya tsallaka zuwa Misra ta mashigar Rafah a ranar 8 ga watan Mayu domin neman lafiya, to amma kwana ɗaya kafin ranar, sai dakarun Isra'ila suka yi wa wurin da Faladinawa suke a Rafah ɗin tsinke inda suka rufe mashigar.
Likitoci dai sun kasa sama wa Amin magani kuma yanzu haka yanayin da yake ciki na ƙara ƙazanta.
Yaron dai ya yi fama kumburin ciki bayan da wani kwanson bam ya faɗa kusa da shi, inda wasu likitoci ke cewa ya samu rauni a cikinsa sakamakon matsalar bam ɗin.
Luba ta ce ɗan nata ya rasa damar tafiya sannan yanayin nasa kullum sai ƙara ƙazanta yake yi.
Yaron mai shekara uku ya dogara ne kan magunguna da allurar jijiyoyi da ake yi masa, kuma soke tafiyar da ya kamata ya yi zuwa Misra kwanaki takwas da suka gabata ya ƙara ta'azzara yanayin da yake fuskanta.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce dakarunta sun karɓe iko da mashigar Rafah, a wani mataki na ƙoƙarin ganin bayan mayaƙan Hamas tare da tunɓuke duk wasu kayan aikinsu da ke kusa da birnin Rafah.
A ranar Talata ne dai ministan harkokin wajen Isra'ila, Israel Katz ya zargi ƙasar Egypt da ci gaba da rufe mashigar amma Egypt ɗin ta ce sojojin Isra'ila ne a yankin suke hana Falasɗinawa ficewa ta mashigar.
Mashigar dai ta kasance hanyar shigar da tallafi sannan hanya ɗaya tilo da mutanen da suke son tserewa tun farko fara yaƙin za su yi amfani da ita.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce yanzu haka kasancewar Kerem Shalom ita ma tana rufe na nufin hanyoyin kai agaji Gaza na rufe.
Tankokin yaƙin Isra'ila na ƙara kutsawa cikin rafah, inda suke umartar Falasɗinawa da su bar yankin zuwa iyakokin da ke kudancin Zirin.
Rafah dai ta ɗaɗe da kasancewar wata mafakar miliyoyin 'yan gudun hijrar Falaɗinawa a tsawon watanni bakwai da aka kwashe ana yaƙi.
“Zan iya rasa ƙafata idan dai har mashigar Rafah ta ci gaba da zama a rufe,” in ji Abdul Karim Al-Dardisi, mai shekara 18, mazaunin Khan Younis da ke kudu maso gabashin Gaza, kamar yadda ya shaida wa BBC.
An dai jikkata Abdul Karim ne watanni uku da suka gabata sannan shi ma na ɗaya daga cikin mutanen da aka daƙilewa damar barin Gaza domin neman lafiya ta hanyar rufe mashigar Rafah.
Dubban mutanen da suka jikkata a Gaza da suka haɗa da yara ba za su iya barin Gazar ba domin neman lafiya, duk da rubuta sunansu da aka yi a jerin sunayen masu yin bulaguro.
Abdul Karim dai yana komawa gidansu ne lokacin da ya ce wani makami mai linzamin da aka harbo daga wani jirgi maras matuƙi ya same shi.
“Hakan ne ya sa , aka yanke ƙafata sannan ɗayar kafar tawa ta samu mummunan rauni," in ji shi.
An kammala shiri tsaf na tafiyarsa da safiyar ranar da dakarun IDF suka rufe mashigar Rafa.
Daga ƙarshe an soke abin da ya tsara dangane da tafiyar tasa. Yanzu dai yana asibitin Turawa da ke kusa da Khan Younis.
"Ina da 'yancin samun lafiya. Ina da asibitocin da zan tuntuɓa a ƙasar waje amma kuma har yanzu ban bar zirin Gaza ba,” in ji shi.
Kamar dai waɗanda suke da raunukan sakamakon rikicin, da dama 'yan Gaza ba za su iya samun kulawar da suke buƙata ba ciki har da waɗanda suke da cutukan da ba kasafai ake ganin irin su ba, sakamaon rufe mashigar ta Rafah
Mounir Al-Dahdouh mai shekara biyu na fama da cutar da ake kira Cornelia de Lange wadda ake ɗuka ta hanyar gado, kamar yadda mahaifinsa ya shaida wa BBC.
Irin waɗannan cutukan na gado na shafar yanayin girman yara sannan kan haifar da haihuwar masu tawaya da rashin gaɓɓai da kuma gadar da matsalolin hanta da zuciya da maraina da kuma jijiyoyin jiki.
Mahaifin Mounir na neman likitoci su aike da ɗan nasa ƙasar waje domin neman magani, to amma sakamakon rufe mashigar Rafah, "dukkan matakan sun ci tura".
Ya ce ɗan nasa na fama da ƙarin matsalar murɗewar jijiyoyin jiki da kuma yawan koke-koke.
Dr Saleh Al-Hams, darektan jinya a Asibitin Turai da ke Gaza wato Gaza European Hospital ya tabbatar da batun ga BBC cewa ikon da sojojin Isra'ila ke da shi a kan mashigar ta Rafah ya samar da tsaiko wajen neman lafiyar jama'a a ƙasashen waje.
To sai dai ya bayyana cewa kusan mutum 40 masu neman lafiya ne ke ficewa ta mashigar kafin a rufe ta. - kusan kaso uku na yawan jama'ar na masu son ficewa kenan.
Al-Hams ya bayyana cewa mutanen da suka ficewa ta mashigar domin neman lafiya ba kawai masu raunuka ba ne, har da masu fama da cutar daji da sauran cutuka masu tsanani.
Kafin yaƙin dai, mashigar Rafah ɗin ta kasance hanya ɗaya tilo ga 'yan Gaza wajen ficewa daga Zirin Gaza. Mashiga ce wadda ba ta ƙarƙashin ikon Isra'ila kafin fara yaƙin.
Harwayau, mashigar ce hanyar shigar da taƙaitaccen tallafi zuwa Gaza tun bayan fara yaƙin.
Inas Hamdan, mai rikon ƙwaryar ofishin darektan hukumar 'yan gudun hijrar Falasɗinu, UNRWAS da ke Gaza, ya shaida wa BBC yadda abubuwa suka taɓarɓare bayan makonni ba tare da shigar da abinci da tallafi da man fetir da kuma magunguna zuwa zirin ba.
"Rumbunanmu na kayan tallafi ya fara zagwanyewa. Akwai buƙatar gaggawa ta kawo agaji a kai a kai musamman bisa la'akari da yadda ake samun sabbin mutanen da ake ɗaiɗaitawa." In ji ta.
Ta tabbatar da cewa kawo yanzu ba agajin da ya shiga zirin ta mashigar Rafah tun bayan rufe mashigar.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta kuma rawaito cewa mamayar Rafah ta jefa sha'anin lafiya da ƙarancin man fetur na yi wa ci gaba da gudanar da ayyukan jinƙai tarnaƙi.
Cogat - hukumar rundunar sojin Isra'ila da ke da alhakin kula da shigar tallafi cikin Gaza, ta ce ana amfani da mashigun Gaza da dama wajen kai kayan agaji sannan an kai litar man fetur 266,000 ta mashigar Karem Shalom a ranar 12 ga watan Mayu.
Ta ƙara da cewa ana kuma kai tallafin ta hanyar jefowa daga jiragen sama, sannan kuma ana sa ran fara shigar da wasu ta hanyar ruwa.