Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Union Berlin ta karɓo aron Fofana daga Chelsea
An wallafa
Ɗan ƙwallon Chelsea David Fofana zai koma taka leda a gasar Bundesliga ta Jamus bayan da ƙungiyar Union Berlin ta karɓi aronsa na tsawon kakar wasa ɗaya.
Ɗan wasan na Ivory Coast mai shekaru 20 ya koma Chelsea ne a watan Janairun bana daga ƙungiyar Molde ta ƙasar Norway.
Sau hudu kacal Fofana ya buga wa Chelsea ƙwallo tun da aka ɗauko shi.
Union Berlin ce ta kammala a matsayin ta hudu a kan teburin Bundesliga a kakar wasan da ta wuce kuma kungiyar a karon farko za ta buga gasar cin kofin zakarun Turai a kakar wasa mai zuwa.