Yadda ake duka da hana Falasɗinawa bacci da abinci a gidajen yarin Isra'ila

Handcuffed hands sit in laps of prisoners sat in a row

Asalin hoton, Israeli Prison Service

Bayanan hoto, Gidajen yarin Isra'ila sun cika maƙil da Falasɗina tun bayan harin da aka kai a watan Oktoban 2024
    • Marubuci, Paul Adams
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Diplomatic correspondent, Jerusalem
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Gargaɗi: Wannan labari na ƙunshe da bayanai wadanda za su iya tayar da hankali

Ƙungiyoyin kare hakkin bil'adama a Isra'ila sun ce yadda ake tsare da Falasɗinawa a gidajen yarin ƙasar ya yi kama da azabtar da ɗan'adam.

Rahoton ƙungiyar B'tselem mai taken "Barka da zuwa Jahannama, na ƙunshe da bayanan da aka samu daga wasu Falsɗinawa guda 55 wadanda aka saki cikin kwanakin nan.

Bayanan sun nuna matsanancin lalacewar al'amura a gidajen yarin tun bayan ɓarkewar yaƙi a Gaza, watanni 10 da suka gabata.

Wannan ɗaya ne daga cikin jerin rahotannin da ake fitarwa, ciki har da rahoton da MDD ta fitar a makon da ya gabata, wanda ya ƙunshi bayanai na cin zarfi da ƙuntatawa da ake yi wa Falasɗinawa.

Ƙungiyar B'tselem ta ce bayanan da jami'anta suka tattara daga waɗanda suka tattauna da su sun yi daidai.

"Dukkaninsu sun faɗa mana abu ɗaya ne," in ji Yuli Novak, shugaban ƙungiyar B'tselem.

"Ana cin zarafi, rikici a kowace rana, duka da azabtarwa, hana mutane bacci da kuma hana su abinci."

Novak ya ce abin ya yi muni.

"Ɗaukacin gidajen yarin Isra'ila sun zamo sansanonin azabtar da Falasɗinawa."

'Cunkoso a gidajen yari'

Tun bayan mummunan harin da Hamas ta kai a Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba, inda aka kashe ƴan ƙasar Isra'ila da na ƙasashen waje kimanin 1,200, yawan Falasɗinawa a gidajen yarin Birtaniya ya nunka zuwa kimanin 10,000.

Gidajen yarin Isra'ila, waɗanda ke ƙarƙashin hukumar gidajen yari ta Isra'ila da kuma wadanda ke ƙarƙashin ikon sojoji sun cika maƙil.

Dakunan gidanjen yarin sun cika sosai, inda wani lokaci akan cunkusa mutanen da dama a ɗakunan da aka tsara domin su ɗauki mutum shida.

Ƙungiyar B'tselem ta bayyana yadda irin wadannan ɗakuna ke cika, ta yadda wasu da ake tsare da su ke kwana a tantagaryar ƙasa, babu katifa babu bargo.

Firas Hassan
Bayanan hoto, Firas Hassan ya ce "rayuwa ta sauya baki ɗaya" tun bayan harin ranar 7 ga watan Oktoba
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Firas Hassan ya kasance a gidan yari tun kafin harin da Hamas ta kai a watan Oktoba.

Ya ce ya ga yadda abubuwa suka taɓarɓare a gidan yarin bayan harin na bara.

A lokacin da muka hadu da shi a yankin Tuqu na Gaɓar Yamma, ya faɗa wa BBC cewa: "Rayuwa ta sauya baki ɗaya."

Mista Hassan ya kasance wanda ya raƙa shiga da fita gidajen yari tun a shekarun 1990, inda sau biyu ana tuhumarsa da kasancewa ɗan ƙungiyar Islamic Jihad, wata ƙungiyar da Isra'ila da wasu ƙasashen Yamma suka ayyana a matsayin ta ƴan ta'adda.

Ya bayyana cewa tabbasa a baya shi ɗan ƙungiyar ne.

Duk da cewa ya saba da zaman gidan yari, amma ya ce bai taɓa tsammanin abin da ya faru da su ba kwana biyu bayan harain 7 ga watan Oktoba.

"Wasu jami'ai 20 sun mana mugun duka, sun rufe fuskokinsu da takunkumi, suna ɗauke da sanduna da karnuka da kuma bindigogi," in ji shi.

"An ɗaure hannuwanmu ta baya, aka ɗaure mana idanu da ƙyalle sannan aka yi mana ɗan karen duka. Jini ya riƙa kwarara a fuskata. Sun yi ta dukan mu tsawon minti 50. Ina ganinsu ta ƙasar ƙyallen da suka rufe mana ido, suna dukanmu suna yi mana bidiyo."

A watan Afrilun ne aka saki Hassan ba tare da yi masa shari'a ba, a wannan lokacin ya rame inda nauyinsa ya ragu da kimanin kilo 20.

Ya shaida wa masu bincike na B'tselem cewa: "na kwashe shekara 13 a gidan yaria baya, amma "ban taɓa fuskantar yanayi irin wannan ba."

Sari Khourieh
Bayanan hoto, Sari Khourieh

Amma ba Falasɗinawa daga Gaza ko Gaɓar Yamma ne kawai suka koka kan irin wannan cin zarafi a gidajen yarin Isra'ila ba.

Ƴan Isra'ila kamar Sari Khourieh, wani lauya balarabe daga Haifa, ya ce irin wannan cin zarafi ya faru da shi.

An tsare Mista Kourieh a gidan yarin Megiddo da ke arewacin Isra'ila na tsawon kwana 10 a cikin watan Nuwamban da ya gabata.

Ƴansanda sun ce wasu daga cikin abubuwan da ya wallafa a shafinsa na facebook sun yaba wa ayyukan Hamas - zargin da ya musanta.

Amma ɗan taƙaitaccen zaman da ya yi - wanda shi ne karonsa na farko a gidan yari - ya kusa sabauta shi.

"Suna yi kamar sun fita daga cikin hayyacinsu," in ji shi, a lokacin da yake tuna zaman da ya yi a gidan yarin Megiddo.

"Babu doka ko ƙa'idoji a gidan."

Khourieh ya ce akan tsame shi a lokutan da ake azabtar da wasu, amma ya kadu da azabar da ake yi wa sauran fursunoni.

"Suna dukansu babau ƙaƙautawa ba tare da wata hujja ba,: in ji shi. "Mutanen suna ihu, suna cewa 'ba mu yi komai ba, bai kamata ku doke mu ba."

Lokacin da ya yi magana da sauran wadanda ake tsare da su ya fahimci cewa ba haka lamarin yake ba gabanin ranar 7 ga watan Oktoba.

A lokacin da ya yi wani taƙaitaccen zama a wani kukukun keɓe fursunoni da ake kira Tora Bora, Khourieh ya ce ya ji wani fursuna da ake bugu yana neman taimakon a ba shi kulawar lafiya a wani ɗakin kurkuku da ke kusa.

Khourieh ya ce likitoci sun yi ƙoƙarin farfaɗo da shi amma ya mutu ba da daɗewa ba.

Rahoton MDD na makon da ya gabata "sanarwar hukumar kula da fursunoni na Isra'ila ya nuna cewa Falasɗinawa 17 da ake tsare da su ne suka mutu tsakanin 7 ga watan Oktoba zuwa 15 ga watan Mayu."

Mun gabatar da zarge-zargen cin zarafin Falasɗinawa ga hukumomin da abin ya shafa.

Sojoji sun "musanta zarge-zargen da ake musu na cin zarafin wadanda ake tsare da su."

Sojojin sun shiada wa BBC cewa "Ƙwararan koke-koke kan saɓa ƙa'idojin aiki da rashin kyawun gidajen yari - ana gabatar da su ne ga ɓangarorin da suka kamata ƙarƙashin rundunar SDF, kuma ana maganace abin yadda ya kamata."

Hukumar gidajen yarin ta ce "ba ta da masaniya game da zarge-zargen da aka gabatar, kuma a iyakar sanin mu hakan bai faru ba."

Israeli prison officers stand outside cell

Asalin hoton, Channel 13

Bayanan hoto, Hukumar gidajen yari ta Isra'ila ta musanta zargin cin zarafin waɗanda ake tsare da su

Tun ranar 7 ga watan Oktoba, Isra'ila ta ƙi bai wa ƙungiyar agaji ta ICRC damar ganawa da Falasɗinawa da ake tsare da, akasin yadda dokar ƙasa da ƙasa ta tanada.

Babu wani bayani da ƙasar ta bayar kan matakin nata, amma gwamnatin Firaiminista Benjamin Netanyahu ta sha nuna damuwa kan gazawar ƙungiyar ICRC wajen gano inda aka ajiye mutanen Isra'ila da ake garkuwa da su a Gaza.

Ƙungiyar tabbatar da ƴancin fararen hula a Isra'ila (ACRI) ta zargi gwamnatin da "karya dokokin ƙasa da ƙasa da gangan".