Rashford ba zai buga wa Man United wasa da Liverpool ba

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Marcus Rashford ba zai buga wa Manchester United wasan Premier ba da za ta kara da Liverpool ranar Lahadi a Anfield, saboda rashin lafiya.

United ba ta yi amfani ba da Rashford, mai shekara 27 a karawa huɗu baya, sakamakon rashin kokari da rashin sa ƙwazo a wajen atisaye da nuna halin ko in kula a tsakanin ƴan wasa.

Tuni sabon kociyan United, Ruben Amorim ya sanar cewar za su tsawaita kwantiragin, Harry Maguire da kaka ɗaya, domin ya ci gaba da taka leda a Old Trafford zuwa 2026.

Sai dai kociyan ya bukaci Maguire ya kara sa ƙwazo a matakin jagora, domin sunyi rashin shugaba da yake jan ragama ƴan wasa a cikin fili.

Amorin ya saka Rashford cikin ƴan wasan da ya kamata su fuskanci Newcastle United, amma sai ya ajiye shi a benci, inda Newcastle ta yi nasara a Old Trafford karo na huɗu a jere da aka doke ƙungiyar kenan.

Napoli mai buga Serie A, itace ake alakantawa da Rashford da cewar za ta ɗauka auro, amma idan za ta iya biyan albashinsa na £300,000 a duk mako.

United tana mataki na 14 a kasan teburin Premier League, wadda za ta fafata da Liverpool ta ɗaya kuma a Anfield.

Tuni ƴan wasan United, Bruno Fernandes da kuma Manuel Ugarte suka kammla hutun dakatarwa.