Al-Ittihad na son Fernandes,Tottenham da Crystal Palace sun kara kaimi don daukar El Khannouss

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Al-Ittihad na son ta sayi Bruno Fernandes na Manchester United kuma tuni suka tattauna da wakilan ɗaan wasan tsakiyar Portugal mai shekaru 30. (Sun), external

Tottenham na kokarin ganin cewa ta sha gaban Crystal Palace a kokarin da take yi wajan siyan ɗan wasan tsakiya na kasar Morocco Bilal El Khannouss daga Leicester bayan ta kasa siyan ɗan wasan gaba na Ingila Eberechi Eze, mai shekara 27. (Africa Foot), external

Watakila Napoli ta kamala cinikin sayan ɗan wasa mai kai hari na Manchester United da Denmark Rasmus Hojlund mai shekara 22 a ranar Litinin domin maye gurbin ɗan wasan mai kai hari na Belgium wanda ya ji rauni Romelu Lukaku mai shekara 32. (Corriere Dello Sport - in Italian), external

Atalanta za ta fafata da West Ham da Nottingham Forest a rige -rigen siyan ɗan wasan tsakiya na Monaco da Faransa Soungoutou Magassa mai shekara 21. (Footmercato - in French), external

West Ham na zawarcin ɗaa wasan tsakiya na kasar Italiya Lorenzo Pellegrini mai shekara 29 wanda aka raba da shi da mukamin kyaftin na Roma (Sky Sport Italia - in Italian), external

Borussia Dortmund na gab da kamala cinikin siyan 'yan wasan Chelsea biyu inda ɗan wasa mai kai hari na Ingila Carney Chukwuemeka mai shekara 21 ya amince da koma taka leda a can a kan yuro miliyan 25, yayin da ɗan wasa baya na Argentina Aaron Anselmino mai shekara 20 ya amince ya koma can a matsayin dan aro . (Sky Sport Germany - in German), external

Roma na sha'awar daukar ɗan wasan baya na Girka Kostas Tsimikas, mai shekara 29, a matsayin aro daga Liverpool. (Giancluca di Marzo - in Italian), external

Kawo yanzu Real Betis na kokarin cimma matsaya da ɗan wasan gefe na Manchester United da Brazil Anthony mai shekara 25 . (Fabrizio Romano), external

Como ta yi watsi da tayin da Tottenham ta yi na yuro miliyan 45 kan ɗan wasan tsakiya na Argentina Nico Paz mai shekara 20. (Nicolo Schira), external

Derby wadda ta lashe gasar Championship ta kulla yarjejeniya da Sturm Graz kan sayen ɗan wasan bayan Scotland, Max Johnston mai shekara 21.(Florian Plettenberg), external