Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wasannin da Real Madrid za ta kara a Champions League 2024/25
Hukumar ƙwallon kafa ta Turai, Uefa ta fitar da jadawalin Champions League da za a fafata a 2024/25, ciki har da wanda Real Madrid za ta kara.
A sabon fasalin da aka sauya a gasar bana, Real Madrid za ta fafata da Stuttgard da Lille da Borussia Dortmund da Milan da Liverpool da Atalanta da Salzburg da kuma Brest.
A kakar da ta wuce Real Madrid ta lashe Champions League na 15 jimilla, bayan da ta yi nasara a kan Borussia Dortmund a Wembley.
Haka kuma a watan jiya Real Madrid ta lashe Uefa Super Cup na bana, bayan da ta yi nasara a kan Atalanta a birnin Warsaw a Poland.
Real ɗin za ta fara wasan zagayen farko ranar Talata 17 ga watan Satumba a Santigo Bernabeu.
Za kuma ta buga wasan karshe a zagayen farko a gasar ta zakarun Turai a gidan Brest ranar Laraba 29 ga watan Janairu.
Jadawalin farko zagayen farko a Champion League
Wasan farko: Real Madrid da Stuttgart (Talata, 17 ga watan Satumba)
Wasa na biyu: Lille da Real Madrid (Laraba, 2 ga watan Oktooba)
Wasa na uku: Real Madrid da Borussia Dortmund (Talata, 22 ga watan Oktoba)
Wasa na huɗu: Real Madrid da Milan (Tatala, 5 ga watan Nuwamba)
Wasa na biyar: Liverpool da Real Madrid (Laraba, 27 ga watan Nuwamba)
Wasa na shida: Atalant da Real Madrid (Talata, 10 Disamba)
Wasa na bakwai: Real Madrid da Salzburg (Laraba, 22 ga watan Janairu)
Wasa na takwas: Brest da Real Madrid (Laraba, 29 ga watan Janairu)