Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Everton ta sake ɗaukar Moyes a matakin kociyanta
David Moyes ya ƙarbi aikin horar da Everton mai buga Premier League a karo na biyu da zai yi aikin kociyanta.
Mai shekara 61, ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka biyu da rabi a Goodison Park, ya maye gurbin Sean Dyche, wanda aka kora.
Everton tana ta 16 a kan teburin Premier da tazarar maki ɗaya tsakaninta da ƴan ukun karshe, bayan cin karawa uku daga wasa 19 da za ta buga kawo yanzu.
Ƙungiyar Goodison Park tana da kwantan wasa da Liverpool, yayin da rashin ƙyawon yanayi ya sa ba a buga karawar ta hamayya ba da ake kira Mersyside Derby.
''Na ji ɗadin kaka 11 da na yi a Everton a baya can, saboda haka nan da nan na amince da tayin da aka yimin a lokacin da aka tuntube ni,'' in ji Moyes.
Moyes ya horar da Everton daga 2002 zuwa 2013 daga nan ya koma Manchester United da Real Sociedad da Sunderland da West Ham har karo biyu.
Ya zauna baya horar da tamaula tun bayan da ya raba gari da West Ham a karshen kakar da ta wuce, wadda ya ci mata Europa Conference League a 2023.