Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko wannan ce kaka mafi muni ga Man United a Premier League?
Kociyan Manchester United, Ruben Amorim ya faɗa cikin fushi cewar watakila wannan ce kaka mafi muni a tarihin ƙungiyar a Premier League.
Hakan ya biyo bayan shan kashin da United ta yi a gida a hannun Brighton da ci 1-3 a Premier League karawar mako na 22 ranar Lahadi.
Hakan ya sa United tana ta 13 a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da maki 26.
Ga jerin ƙididdigar rashin ƙoƙarin Manchester United a shekarun baya:
Bayan da Brighton ta yi nasara a kan United a Old Trafford, karo na shida ke nan da aka doke ƙungiyar a gida a wasa na 12 tun bayan 1893/94.
United ta ƙare a ƙarshen teburi, lamarin da ya kai ga ta bar buga gasar ta rukunin farko a lokacin da ake kiranta da sunan Newton Heath.
A shekarar 1914/15 aka sauya sunan ƙungiyar zuwa Manchester United, wadda ta ƙare a gurbi na 18 a cikin ƙungiyoyi 20 - da maki 30 a karawa 38.
Wani rashin kokarin da United ta yi a kakar shi ne lashe wasa tara wato kaso 24 cikin 100, idan ka kwatanta da 32 cikin 100 a kakar nan.
Sau biyar jimilla United tana zuwa 'relagation' a Ingila, wadda ta yi ta karshe a 1921/22 da maki takwas da ƙara yin ta karshe a 1930/31 da maki 10.
Ta taɓa komawa buga gasar rukunin farko da faɗuwa daga wasannin a 1935 da kuma 1938 - kaka ta baya-baya ita ce 1973/74 lokacin da ta kare ta 21 daga ƙungiyoyi 22.
Wannan ce kaka mafi muni a United da take ta 13 a kan teburi tun bayan 1989/90 da take kan irin wannan matakin.
Ƙungiyar da Amorim ke jan ragama tana da maki 26 daga wasa 22, wato tazarar maki takwas daga rashin kwazo a gasar baya.
Ta haɗa maki 34 a 2019/20 a irin wannan lokacin, amma sai ta kara ƙwazo da ta ƙare a mataki na uku da maki 66.
Bayan haɗa maki 35 daga karawa 22 a bara, United ta ƙare a mataki na takwas da maki 60 da lashe FA Cup ƙarƙashin Erik ten Hag.
Haka kuma United ta kare kakar Premier League a mataki na shida karo uku da yin ta bakwai a 2013/14.
United ta ɗauki kofin Premier League 13 daga kaka 21 ƙarƙashin Sir Alex Ferguson, wannan ce kaka ta 12 rabon ta da lashe babban kofin tamaula ta Ingila, tun bayan da ya yi ritaya.