A karon farko Arsenal ta doke Man United wasa huɗu a jere a Premier

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Arsenal ta doke Manchester United 2-0 a wasan mako na 14 a gasar Premier League da suka fafata ranar Laraba a Emirates.

Gunners ta ci ƙwallayen bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu, inda Timber ya fara cin ƙwallo, sannan Saliba ya zura na biyu a raga.

Wannan shi ne karon farko da Arsenal ta doke United wasa hudu a jere a Premier League a tarihi.

Kuma wasa na 500 da Gunners ta yi a Emirates a dukkan fafatawa.

United ta fuskanci Arsenal da koci biyar a bayan nan da suka haɗa da Jose Mourinho (Afirilun 2018) da Ole Gunnar Solskjaer (Janairun 2019) da Michael Carrick (Disamba 2021) da kuma Erik ten Hag (Satumbar 2022) da Ruben Amorim (Disambar 2024)

Ranar Lahadi Arsenal za ta je gidan Fulham a Premier League, sannan ta karbi bakuncin Monaco a Champions League ranar Laraba.

Ita kuwa United za ta karɓi bakuncin Nottingham Forest ranar Asabar a Premier League, sannan ta je Viktoria Plzen a Europa League ranar Alhamis.

Wasa huɗu a jere da Arsenal ta doke Man United:

A kakar 2024/25

Premier League Laraba 04 Disamba 2024

  • Arsenal 2 - 0 Man Utd

A kakar 2023/24

Premier League Lahadi 12 ga watan Mayun 2024

  • Man Utd 0 - 1 Arsenal

Premier League Asabar 3 ga watan Satumba 2023

  • Arsenal 3 - 1 Man Utd

A kakar 2022/23

Premier League Lahadi 22 ga watan Janairu 2023

  • Arsenal 3 - 2 Man Utd

Premier League Lahadi 4 ga watan Satumba 2022

  • Man Utd 3 - 1 Arsenal