Yadda rage kuɗin ruwa a Najeriya zai shafi rayuwarku

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

A ranar Talata Babban Bankin Najeriya, CBN ya sanar da rage kuɗin ruwa na bayar da bashi a ƙasar da rabin maki, daga 27.5% zuwa 27%.

Wannan ne karo na farko da bankin ya ɗauki irin wannan mataki a cikin shekara biyar. To amma abin da matsakaicin ɗan Najeriya zai tambaya shi ne ta yaya abin zai shafe shi?

Masana tattalin arziƙi da hada-hadar kuɗi na ganin cewa rage kuɗin ruwan zai kawo sauyi a ɓangarorin tattalin arziƙin ƙasar da dama ta yadda zai shafi mutunen da ke ƙasa.

To amma wani masanin tattalin arziƙi da ke zaune a birnin Legas, Shu'aibu Idris Mikati ya ce sun yi tsammanin CBN zai rage kuɗin ruwa fiye da haka.

"Tun a cikin watanni da suka gabata hauhawar farashin kaya ta ragu mun yi tunanin cewa lokaci ya yi da Babban Bankin Najeriya zai rage kuɗin ruwa.

"Tunaninmu shi ne za su rage maki ɗaya daga kuɗin ruwan, to amma sai suka rage rabi," in ji Mikati.

Wane sauyi za a gani sanadiyyar rage kuɗin ruwa?

Tun bayan sauye-sauyen ɓangaren kuɗi da gwamnatin Shugaba Tinubu ta kawo - wanda ya ta'azzara tashin farashin kaya da rage darajar naira - ƴan Najeriya ke ɗari-ɗari da duk wani mataki da gwamnatin za ta ɗauka a ɓangaren na kuɗi.

To sai dai Mikati ya ce matakin CBN din na baya-bayan nan zai iya yin kyakkyawan tasiri ga tattalin arziƙi ta yadda ƴan Najeriya za su iya samun sauƙi.

Darajar naira ta ɗaga:

Tasiri na farko da za a ce an fara gani shi ne yadda darajar naira ta ɗaga idan aka kwatanta da dalar Amurka.

An canzar da nairar kan N1,487.36 kan dala ɗaya ranar Talata a kasuwar canji ta hukuma.

Inda aka rufe kasuwar canjin kuɗi ta jiya Talata nairar tana da ƙarin darajar kashi 0.08 idan aka kwatanta da 1,488.60 da aka canzar da ita kafin haka, kamar yadda bayanan CBN suka nuna.

Ƙarin farashin gangar ɗanyen man fetur:

Kazalika, shi ma farashin ɗanyen man fetur ya ɗan ƙaru zuwa dala 67.82 zuwa ƙarfe 5:00 na safiyar Laraba - kwana daya bayan ragin kudin ruwan - inda ya ƙaru da santi 19 - ko kuma kashi 0.3 cikin 100 - kan kowace ganga ɗaya.

Fetur shi ne babbar hanyar samun kudin shiga na Najeriya, kuma raguwa ko kuma tashin farashinsa ne ke tantance abin da zai tantance yawan kuɗin da ke shiga lalitar gwamnati, wanda da shi ne gwamnatin ke tafiyar da ayyukanta.

Saukar farashi:

Idris Mikati ya ce rage kuɗin ruwa da CBN ya yi na nufin cewa bankunan kasuwanci na Najeriya za su rage yawan kuɗin ruwa da suke karɓa daga wurin mutane da kamfanonin da suka ci bashi a wurinsu.

"A ƙa'ida idan ƴan kasuwa da masana'antun da ke cin bashi daga bankuna sun samu rangwame a kuɗin ruwan da ake karɓa daga wurinsu, ya kamata su rage kuɗin kayan da suke sarrafawa suna sayar wa jama'a," in ji Mikati.

Ya ƙara da cewa hakan zai sanya farashin kayan da al'umma suke saya a kasuwanni ya ragu.

Tashin farashi na daga cikin manyan matsalolin da al'ummar Najeriya ke kokawa a kai tun bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin Tinubu ta yi a farkon kama aiki.

Sai dai a baya-bayan nan alƙaluma daga hukumar ƙididdiga ta ƙasar sun nuna cewa an samu ragin hauhuwar farashin.

Riba a ladar ajiya a banki:

A ɗaya ɓangaren kuma masanin ya ce bankuna za su ci gaba da biyan masu ajiya a wurinsu kuɗin ruwa daidai da alƙawarin da suka ƙulla a baya.

Hakan na nufin yayin da a hukumance bankuna za su rage kudin ruwa da suke karba daga wurin wadanda suka ci bashi, amma su masu ajiya ba za a rage komai daga cikin ladar da ake ba su fa.

Ko rage kuɗin ruwa zai shafi bashin gidaje?

Masanin tattalin arziƙin ya ce "a duk lokacin da CBN ya rage kuɗin ruwa, duk wani wanda ke hulɗa da banki ta hanyar cin bashi, hatta bashin gida, to abin zai shafe su.

"Yawanci, bankuna idan za su bayar da bashi sukan yi la'akari da kuɗin ruwa mafi ƙaranci na Babban Bankin Najeriya, kuma a duk lokacin da Babban Bankin ya rage ko ya ƙara, to shi ma kuɗin ruwa da za a biya zai ragu ko ya ƙaru," a cewar Mikati.

Saboda haka daga bayanin masanin, mutanen da suka karɓi bashin gida, a karon farko cikin shekara biyar za su samu rangwame a kuɗin ruwa da suke biya.