Liverpool ta lashe Premier League na 20 a kan Tottenham

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Liverpool ta lashe Premier League na 2024/25 na 20 jimilla, bayan da ta caskara Tottenham 5-1 ranar Lahadi a Anfield.

Tottenham ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Dominic Solanke minti 12 da fara wasa, sai dai minti huɗu tsakani Liverpool ta farke ta hannun Luis Diaz, sannan Mac Allister ya kara na biyu.

Daf da za su je hutu ne ƙungiyar Anfield ta kara na uku ta hannun Cody Gakpo, sai Mohamed Salah ya kara na huɗu, sannan Tottenham ta ci gida ta hannun Destiny Udogie.

Kenan Liverpool ta samu damar ɗaukar kofin Premier League na bana na 20 jimilla, iri ɗaya da yawan na Manchester United.

Liverpool ta samu damar lashe kofin bana, saura wasa huɗu-huɗu a kare kakar nan, bayan da Arsenal ta tashi 2-2 da Crystal Palace ranar Laraba a Emirates.

Liverpool ta ɗauki Premier na bana da maki 82, bayan cin wasa 25 da canjaras bakwai aka doke ta wasa biyu.

Arsenal ce ta biyun teburi mai maki 67, bayan cin wasa 18 da canjaras 13 da rashin nasara uku a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Liverpool ta yi wannan ƙwazon karkashin sabon koci, Arne Slot da ta dauka kan a fara kakar nan, wanda ya maye gurbin Jurgen Klopp, wanda ya yi ritaya.

Tun farko Liverpool ta yi fatan lashe kofi huɗu a kakar nan, sai dai an yi waje da ita a League da FA Cup.

Haka kuma ta yi ban kwana da Champions League na kakar nan, bayan da Paris St Germain ta yi waje da ita a zagaye na biyu.

Tuni dai an samu gurbi ukun da suka yi ban kwana da Premier League da za su koma buga Championship a baɗi da suka haɗa da Ipswich da Leicester da kuma Southampton.

Yanzu inda ake tata burza shi ne gurbin da za su wakilci Ingila a baɗi a gasar zakarun Turai.

Ƙungiya biyar ce za ta wakilci Ingila a baɗi a Champions League, yayin da watakila su zama shida da zarar Manchester City ko Tottenham ta lashe Europa League.

Manchester United da Tottenham duk sun kai zagayen daf da karshe a Europa League.