Me ya sa China da Rasha ke ƙoƙarin sasanta Isra'ila da Falasɗinu?

    • Marubuci, Paula Rosas
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Mundo
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 7

China da Rasha sun daɗe suna goyon bayan fafutikar Falasɗinawa.

Amma cikin ƴan kwanakin nan, China da Rasha sun fara komawa masu shiga tsakani a yaƙin na Isra'ila da Falasɗinu tun daga bara da wannan yaƙin ya ɓarke.

A watan Yuli, ƙungiyoyin Hamas da Fatah da wasu ƙungiyoyin Falasɗinawa sun ƙulla wata yarjejeniya a zaman da suka yi a birnin Beijing domin samar da "gwamnatin riƙon ƙwarya ta haɗin kai" domin gyara Gaza bayan yaƙin ya lafa. Haɗakar ƙungiyoyin sun sake zama a Moscow a Fabrairu domin sabunta yarjejeniyar.

China da Rasha na da alaƙa mai kyau da wasu ƙasashen yankin irin su Iran, Syria da Turkiyya. Amma ba kamar Amurka ba, su ba sa kallon Hamas a matsayin ƙungiyar ta'addanci, shi ya sa suke iya zama su tattauna da ita.

Amma shin tattaunawar za ta haifar da ɗa mai ido? masana da BBC ta zanta da su sun ce da kamar wuya. Amma duk da haka tambayar da ake yi ita ce, me China da Rasha suke so a wannan yunƙurin na samar da mashala?

Akwai manufofi guda biyu: samun ƙarfin iko a duniya, sai kuma adawa da Amurka da wasu ƙasashen yamma.

Daga Mao zuwa Xi Jinping

Tun bayan kafa sabuwar ƙasar China a shekarar 1949, giwar yankin ta Asia take tausayin Falasɗinawa.

Wanda ya assasa ƙasar, Mao Zedong, yana kallon Isra'ila ne kamar yadda yake kallon Taiwan: wakiliyar ƙasashen yamma domin cigaba da danniya.

Goyon bayan bai tsaya a magana ba, Mao, wanda ya daɗe yana goyon bayan fafutikar ƴantar da ƙasashe a faɗin duniya, ya sha ba Falasɗinawa makamai.

An samu sauyi a harkokin wajen China bayan Deng Xaoping ya hau karagar mulki a shekarar 1978.

Amma da Xi Jinping ya hau mulki a 2012, Mista Aboudouh ya ce, "Xi yana gyara a tsare-tsaren harkokin wajen ƙasar, domin cimma wasu muradun China, sannan zai samu wannan damar a yaƙin Isra'ila da Falasɗinu."

Daga Stalin zuwa Putin

Alaƙar Rasha da Falasɗinu ta samo asali ne ta wata hanyar daban. Lokacin da Isra'ila ta sanar da samun ƴancinta a shekarar 1948, ƙasashen Soviet Union, ƙarƙashin Josef Stalin, na cikin ƙasashen da suka fara amincewa da ita a duniya.

Daga baya sai Isra'ila ta ƙi zama ƴar gurguzu, wanda hakan ya sa a tsankakanin shekarun 1950, tsohon jagoran Soviet, Nikita Khrushchev ya fara juya alaƙarsa zuwa ga Larabawa.

"Fafutikar Falasɗinawa yana da muhimmanci a wajen Rasha, saboda Amurka tana goyon bayan Isra'ila ne, sannan goyon bayan Soviet ga Falasɗinawa ya ƙara mata farin jini a yankin Larabawa," in ji farfesa Katz.

“Ba za su so goyon bayan ya haɗa su rikici da Amurka ba, sannan kuma ba su taɓa zama masu adawa da Isra'ila ba," in ji Mista Katz.

Amma tun bayan rushewar haɗakar ƙasashen Soviet, sai Rasha ta fara sassauta wa Isra'ila.

Tun lokacin ne Rasha take ta ƙoƙarin samar da daidaito tsakanin alaƙarta da Rasha da kuma goyon bayan Falasɗinawa.

Sabon tsarin tafiyar da duniya

A duniya China ce tafi sayen fetur, sannan kusan rabin man tana sayowa ne daga ƙasashen Gabas ta Tsakiya. Shin wannan na nufin tana shiga tsakani ne a yaƙin na Falasɗinu da Isra'ila domin tattalin arzikinta? Ahmed Aboudouh na Chatham House ya ce ba haka ba ne.

"Ƙasashen Larabawa da dama suna da alaƙa mai kyau da Isra'ila, sannan sauran kuma, kamar Saudiyya, suna shirin yin hakan idan yaƙin Gaza ya lafa. China ta fahimci haka, shi ya sa take taka tsan-tsan," in ji shi.

Wataƙila China na ƙara shiga lamarin ne domin adawarta da Amurka, da kuma ƙoƙarin nuna wa duniya cewa ita mai shiga tsakani ne.

"China ba ta da masaniya a kan yadda za a magance rikicin Falasɗinu da Isra'ila, kuma ba ta da wani abu da take son cimmawa idan an samu maslahar," in ji Mista Aboudouh.

Kawar da hankali daga yaƙin Ukraine

Ita kuma Rasha, yaƙin Hamas da Isra'ila ya taimaka mata wajen ɗauke hankalin duniya daga yaƙin da take yi da Ukraine, kamar yadda farfesa Katz ya bayyana.

Ahmed Aboudouh na Chatham House ya ce ƙoƙarin shiga tsakani da Rasha ke yi bai rasa nasaba da yunƙurin wanke kanta daga ware ta da ƙasashen yamma suka yi bayan ta far wa Ukraine da yaƙi.

Rasha ba ta ɗauki Hamas - wadda ta ƙwace iko da Gaza a shekarar 2007 - a matsayin ƙawar amana ba saboda ra'ayin Musulunci da take da shi, amma hakan bai hana Rasha aiki da ƙungiyar ba.

Hakan ya yi amfani. Lokacin da Rasha ta kutsa Gerogia a 2008, "da Hamas da Hezbollah duk sun goyi bayan Rasha ne a kan Georgia," in ji Katz.

Masana sun yi amannar cewa duk da alaƙar da ke tsakanin Hamas da Rasha, babu wata alamar Rasha na ba ƙungiyar makamai, saboda fargabar ita ma Isra'ila za ta iya fara ba Ukraine makamai.

Hanyoyi daba-daban

Duk da cewa wasu daga cikin muradunsu sun zo ɗaya, musamman na rage ƙarfin ikon Amurka a Gabas ta Tsakiya, amma da China da Rasha suna amfani da hanyoyi daban-daban ne.

Da farko, ita Rasha ta shiga harkokin soji a yankin, kamar yadda ta yi a yaƙin Syria - abin da China ba ta yi.

A daidai lokacin da China take son gyara yadda ake gudanar da wasu harkoki a Gabas ta Tsakiya domin su yi daidai da muradunta, ita kuma Rasha tana so ne ta yi garambawul baki ɗaya domin cimma nata muradun, kamar yadda Aboudouh ya bayyana.

Ya ce China za ta so a samu maslahar yaƙin ta hanyar samar da ƴantacciyar Falasɗinu, ta yadda zai zama China na da wani ƙarfin iko faɗa a ji.

Ita Rasha tana bi a hankali ne. Ba wai tana so yaƙin na Isra'ila da Falasɗinu ya ƙare baki ɗaya ba ne, ta laɓe ne da sunan neman maslaha.

"Idan har yaƙin ya ƙare, da Isra'ila da Falasɗinu babu wadda za ta cigaba da buƙatar Rasha. Za su koma neman hanyoyin haɓaka tattalin arzikin ƙasashensu ne, wanda dole ko dai su koma ga ƙasashen yamma ko su bi China, ko su haɗa duka."