Bikin ranar tagwaye da cashewar birrai a mota a cikin hotunan Afirka

Kyawawan tagwaye sun tsaya daukar hoto a ranar Tagwaye da aka gudanqr wato  World Twins Festival 2024, a Igbo-Ora - ranar Lahadi 12 aoktoba 2024

Asalin hoton, Olympia De Maismont/AFP

Bayanan hoto, A ranar Lahadi ne aka gudanar da bikin ranar tagwaye a Najeriya, wanda ake kira, Igbo-Ora.
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Wasu daga cikin ƙayatattun hotunan Afirka da na 'yan nahiyar a wasu sassan duniya cikin makon da ya gabata

Masu sauya a na Kayan kawa, daga kungiyar Ajao Lokacin da suke kayatar da masu kallo a ranar Alhaji’s 11 Oktoba 2024 a birnin Karachi na Paskitan.

Asalin hoton, Shahzaib Akber/EPA

Bayanan hoto, A ranar Alhamis, masu zayyanar kayan ƙawa na ƙungiyar Ajao daga Afirka ta Kudu suka ƙayatar da masu kallo a wurin bikin kalankuwar birnin Karachi na ƙasar Pakistan.
Hoton iyalan giwaye a wurin sha karawa ma Aberdare, da ke Mweiga, a yankın Nyeri a Kenya - Litinin 14 Oktoba 2024.

Asalin hoton, Thomas Mukoya/Reuters

Bayanan hoto, Waɗannan wasu iyalan giwaye ne, suka yi tsayuwar Nutsuwa tamkar sun san ana ɗaukarsu hoto a wurin shaƙatawa ma Aberdare a ƙasar Kenya.
Wani mutum ne ke gwada kwanjinsa a wurin gasar masu gwada Kwan ji da aka guSarit da ke tsakiya birnin Nairobi, ranar Asabar 11 Oktoba 2024 w gundumar Sarıtaş

Asalin hoton, Thomas Mukoya/Reuters

Bayanan hoto, A ranar Asabar, wani matashi ke gwada ƙwangi a wurin gasar nuna murɗewar jiki na maza da mata a gabashin Afirka
Masu gwajin kWa ji - Asabar 13 Oktoba  2024.

Asalin hoton, Gerald Anderson/Getty Images

Bayanan hoto, Gasar na da za tsauri sosai, saboda kowane ɗan takara sai ya nuna irin yadda jikinsa ya mummurɗe.
Mutum-mutumin wani sarki, da aka bake kolin shi a fitaccen wurin adana kayan tarihi na Giza a kaşar Masar, a ranar Talata 15 Oktoba 2024.

Asalin hoton, Mohamed Hossam/EPA

Bayanan hoto, A ranar Asabar an baje kolin mutum-mutumin wani sarki a ranar bikin buɗe gidan adana kayan tarihi da ke Giza a ƙasar Masar
Ranar abinci ta duniya, da aka gidan at a burnun Lagos a Najeriya, karkashin kulawar Ma’aikatar aikin gona ta Kaşar. A ranar Laraba 16 Oktoba 2024.

Asalin hoton, Adekunle Ajayi/Getty Images

Bayanan hoto, Washe gari, masunta suka yi holen manyan kifi nau’in karfasa da suka kama a ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin abinci.
Birrai nau’in Chacma su na wasa Alan wata mota, ranar Litinin 14 Oktoba 2024, a Afurka ta Kudu.

Asalin hoton, Nic Bothma/Reuters

Bayanan hoto, A ranar Litinin wasu birrai huɗ suka yi dirar mikita a kan wata mota suna wasa a unguwar Capri da ke Cape Town na Afirka ta Kudu.
Biri nau’in Chacma ya na tsintar abinci a bola a Cape Town, Afirka ta Kudu ranar Litinin 14 Oktoba 2024.

Asalin hoton, Nic Bothma/Reuters

Bayanan hoto, Amma ɗaya daga cikin su ya gwammace cin abinci maimakon wasa.
Mai saida Kayan marmari a wurin sha karawa ma Tastour a kaşar Tunisia, ya jera dan içen Ruman a ranar Lahadi 13 Oktoba 2024, ya kayata wurin da alamar zuciya da ke nuna soyayya.

Asalin hoton, Mohamed Messara/EPA

Bayanan hoto, Can a ƙasar Tunusia wani mutum ne ya jera ɗan itacen ruman ta hanyar zaɓen zuciya guda biyu, a wani mataki na tallata hajarsa ga masu yawon buɗe ido.