Hamas ta ce ta dakatar da sakin ƴan Isra'ila da ta yi garkuwa da su

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar Hamas ta ce ta dakatar da sakin sauran Isra'ilawan da ke hannunta, sai yadda hali ya yi.
Sanarwar da bangaren sojin Hamas din ya fitar ta ce "fiye da mako uku, shugabacin ƙungiyar na bibiyar yadda maƙiya suka gaza cika ka'idojin yarjejeniyar da suka cimma", a cewar Hamas din.
"Karya wannan ƙa'ida, har da jinkirta dawowar wadanda suka rasa muhallansu zuwa arewacin Gaza, inda ake fakon su tare da harbin su, da harba musu bama-bamai, a yankuna daban-daban na Gaza, wanda hakan ke nuni da yadda suka gaza ƙyale ayyukan jinƙai, da sauran yarjejeniyar da suka cimma tunda farko.
"Baya ga nan, dakarun na Hamas tun farko sun mutunta wannan alkawari da aka yi.
Haka kuma sanarwa ta Hamas ta ce "sakin ƙarin wasu masu rajin kafa kasar Yahudawa a ranar Asabar, 25 ga watan 2025, sun dakatar da shi, sai nan gaba, yayin da suke jiran maƙiya, za su fara mutunta yarjejeniyar da aka cimma da aka fara aiwatarwa makkonin da suka gabata.
"Muna sake jadada aniyarmu ta ci gaba da mutunta dukkan yarjejeniya da ka'idojin da aka gindaya, idan har masu mamayar suka bi su sau da kafa".
An shirya sakin ƙarin wasu Isra'ilawa uku a ranar Asabar.
A shirye dakarun Isra'ila suke a Gaza - Kartz
Isra'ila ta mayar da martani dangane da sanarwar da Hamas ta fitar cewa ta dakatar da sakin mutanen da take garkuwa da su .
Wata sanarwa da ministan tsaron Isra'ila ya fitar ta ce " sanarwar dakatar da sakin waɗanda Hamas ke garkuwa da su ya saɓa yarjejeniyar tsagaita cimma wutar da ta musayar fursunoni da aka amince," in ji Israel Katz:
"Na bai wa dakarun IDF umarnin kasancewa cikin ko-ta-kwana dangane da duk wani da ka iya biyo ba a Gaza domin kare al'umma.
"Ba za mu bari a maimaimata abin da ya faru ranar 7 ga watan Oktoba ba.."
Dakarun Isra'ila sun janye daga iyakar da ta raba Gaza gida biyu

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Gabanin sanarwar ta kungiyar Hamas na dakatar da sakin sauran Isra'ilawan da ta yi garkuwa da su, wasu rahotanni sun nuna cewar dakarun Isra'ila sun janye daga iyakar Netzarim yankin da sojoji suka datse arewaci da kudancin Gaza.
Ɗaruruwan Falasdinawa da ke cikin motoci da amalanke dauke da katifu, da sauran kayayaki, ne suka fara komawa Gaza bayan da dakarun suka janye, daga inda suka lalata.
Janyewar dakarun Isra'ila na daga cikin cika yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a ranar 19 ga watan Janeru, inda aka saki Isra'ilawa 16 da Falasdinawa 566 kawo yanzu.
Zuwa karshen zangon farko na tsagaita wutar nan da mako uku daga yanzu, 33 daga cikin wandan da aka yi garkuwar da su, da dauraru 1,900, ana sa ran za a sako dukkanin su. Sai dai Isra'ila ta ce 8 daga cikin 33 daga cikinsu sun mutu.
Hamas ta yi garkuwa da mutum 251, sannan ta kashe kusa mutum 1, 200 a lokacin da ta kaiwa Isra'ila hari a ranar 7 ga watan Octoban 2023, wanda shi ne ya janyo yakin na Gaza.
A cewar ma'aikatar lafiya ta Hamas, kimanin Falasdinawa 48, 189 aka halaka a hare-haren da Isra'ilan ta kai. Sannan Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin biyu bisa uku na gine gine da ke Gaza sun lalace ko kuma sun rushe sakamakon hare-haren da Isra'ila ta kai.
A ranar Lahadi an ga gwammon Falasdinawa na wucewa ta iyakar Netzarim, kuma mafi akasarinsu na yin arewaci Gaza don ganin abubuwa da suka faru bayan sun bar gidajensu.
Wani mazaunin birnin Al-Maghraqa da ke arewacin Netzarim, ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na AFP cewa "mun ga bala'i, da rushe rushe masu mutukar tayar da hankali. Isra'ila yan kama guri zauna sun lalata gidaje, Shaguna, masalatai, jami'o'i, da kotuna" a cewarsa .
Wani mai shekaru 57, da aka turasasa masa barin gidansa, fiye da shekara guda, a kudancin Gaza, wato birnin Khan Yunis, ya ce ya shirya 'kafa tanti don amfanin na da na iyalina'.
"Ba mu da wani zabi" a cewar sa.
Mahmoud al-Sarhi, Bafaladsine ne da ya rasa matsuguninsa, ya shaidawa kamfanin dillanci labarai na AFP cewar "zuwan sa Netzarim tarar mutuwa ne, amma banda a safiyar da ya isa wajen".
Ya ce wannan shi ne "karon farko da na ga yadda a lalata gidanmu", yana mai nuna gidansa da ke kusa da yankin Zeitun.
"Gaba daya yankin an lalata shi. Bazan iya zama a nan ba," a cewar sa.
Kimanin mazauna arewacin Gaza 700, 000 ne suka tsere zuwa kudancin yakin, tun a farkon fara yakin, a lokacin da sojijin Isra'ila, suka umarci da dubban Falasdinawa da su bar yankunansu gabanin su kaddamar da kai hari kan yankin Falasdinawa.
Da dama daga cikin wadan da suka rasa matsugunensu, an sake tilasta musu, sauya wuri har sau biyu, bayan da dakarun Isra'ila sun kutsa kudancin Gaza.
An kuma hana su, komawa gidajensu, ta iyakar Netzarim, zuwa Iyakar Gaza da Isra'ila zuwa bahar Rum.
Sai dai dakarun Isra'ila sun dan janye daga yammacin iyakar a watan da ya gabata, kuma hakan ya baiwa Falasdinawan damar bi ta titin Rashid da ke gabar teku, yayin da suke tsallaka zuwa areawacin Gaza.
Haka kuma wadanda ke cikin ababen hawa, suka bi titin Salah al-Din, sannan sai jami'an tsaro na kwantaragi na Amurka da Masar ke tantance su.
Dakarun tsaro na Isra'ila ba su kai ga fitar da wani jawabi ba, kan janyewar tasu daga gabashin iyakar ba a ranar Lahadi, wanda za su bar ta a karkashin ikon masu kula da iyaka na Gaza, ammam banda titun da suka katse fiye da rabinsa.
Jaridar Haaretz ta ce Ministan harkokin cikin gida na Hamas a Gaza, ta yi kira ga mutane da "su kiyaye tare da ci gaba da bin ka'idoji kula da kariya".
Janyewar dakarun na Isra'ila na zuwa ne yayin da ake sa ran wakilan Isra'ila za su isa Qatar, wadda ke shiga tsakanin bangarorin biyu a yakin da suke da Gaza.
A baya dai gwamantin Isra'ila ta ce wakilan na ta za su tattaunawa ne kan "abubuwa masu sarakkiya" da suka shafi tattaunawar farko da ke kushe da zaman lafiya na farko, maimakon irin kalubalen da za a iya fuskanta a zango na biyu na tattaunawar, wadda ake sa ran cewar zata haifar da zaman lafiya na din-din-din, da musayar fursunonin da ke Gaza, don sako karin wasu Falasdinawa, da janyewar dakarun Isra'ila daga Gaza baki daya.

Asalin hoton, Getty Images
Sai dai hakan na iya samuwa ne bayan da Firai ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, wanda ya zama shugaban wata kasa da ya fara ganawa da shugaban Amurka Donal Trump, bayan da ya koma fadar White house.
A yayin balaguron na sa, a wani sauyi da baa saba gani ba, a manufar Amurka kan Gaza tsawon shekaru, Trump ya yi kira da a kori daukacin fararen hular da ke yankin da samar da ci gaban a abun da suka kira "Kayatacen gabar Teku da ke Gabas ta Tsakiya".
A yayin zaman sa da 'yanmajalisar zartarwarsa, tun bayan dawowarsa daga Amurka, Netanyahu ya ce Trump ya zo da "wani abu daban, da ya fi kwantawa Isra'ila a rai".
"Wani tunaini ne, na juyin juya hali, muna tattaunawa akai" an jiyo shi yana mai bayana hakan a yayin da ya ke karanta jawabinsa a yayin zaman majalisar zartarwar ta sa. "Trump na da karfin aniyar ganin an aiwatar da hakan, wanda ya sake bude damarmaki masu yawa gare mu."
Bukatar ta Trump, wadda ka iya zama babban laifi a dokar kasa da kasa, kuma tuni kasashen duniya, ciki har da na larabawa suka yi wasti da ita.
A ranar Asabar, ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila ta ce ba zata amince da "dukkan wani nau'in take hakkin Falasdinawa, da dukkan wani yunkuri na rabasu da mastugunensu, inda ta zargi Isra'ila da "kawar da wata kabila".
Masar ita ma ta yi watsi da shawarar ta dauke al'ummar Falasdinawan, inda ta yi kira da gagguta kiran wani taron kasashen larabawa a ranar 27 ga watan Fabarerun da muke ciki, don tattunawa kan abin da ta kira halin da falasdinawa ke ciki mai "matukar mahimmanci".










