Matakan da aka bi wajen cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

Woman protesting against the government and showing support for the 7 October hostages holds up both hands, with the words "Stop the War" written on her palms, as demonstrators with banners stand in the background

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wata mai zanga-zanga a Isra'ila ta yi kiran a kawo ƙarshen rikicin a farkon watan Janairun 2025
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Isra'ila da Hamas sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta da sakin mutanen da aka yi garkuwa da su.

Yarjejeniyar ta faru ne bayan kwashe watanni 15 ana fafatawa tsakanin Isra'ila da Hamas.

Rikicin na Gaza ya samo asali ne bayan da ɗaruruwan ƴan ƙungiyar Hamas suka far wa yankin kudancin Isra'ilar da ke iyaka a ranar 7 ga watan Oktoban 2023 inda suka kashe ƴan Isra'ilar 1,200 sannan suka yi garkuwa da mutum 250.

Isra'ila ta mayar da martani da ƙarfin soji inda suka fara da hare-haren sama sannan suka biyo shi da kutsawa cikin ƙasar bayan ƙaddamar da yaƙi a ranar 27 ga watan Okotba.

Kuma tun bayan nan ne Isra'ila ke ta kai hare-hare a Gaza ta sama da ƙasa da ruwa, a daidai lokacin da ƙungiyar Hamas ke ci gaba da mayar da martani ta hanyar harba rokoki zuwa cikin Isra'ila.

Isra'ila ta kashe fiye da Falasɗinawa 46,700 inda mafi yawansu fararen hula ne da suka haɗa da mata da yara, kamar yadda alƙaluman ma'aikatar lafiya ta Gaza ta bayyana.

Ga wata matashiya kan wasu manyan abubuwan da suka faru dangane da yarjejeniyar.

Wani yaro ɗan Falasdinu sanye da riga launin rawaya, zaune a kan baraguzan gine ginen da hare haren Israila su ka rusa a birnin Gaza, a ranar 16 ga watan Janairun 2025

Asalin hoton, Reuters

Abubuwan da suka janyo cimma tsagaita wutar

2023

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

7 ga watan Oktoba: Ɗaruruwan ƴan ƙungiyar Hamas suka far wa yankin kudancin Isra'ila da ke iyaka a ranar 7 ga watan Oktoban 2023, al'amarin da ya yi sanadiyyar mutuwar ƴan Isra'ilar 1,200 sannan suka yi garkuwa da mutum 250.

27 ga watan Oktoba: Isra'ila ta mayar da martani da ƙarfin soji inda ta fara da hare-haren sama sannan ta bi shi da kutsawa cikin ƙasar bayan ƙaddamar da yaƙi a ranar 27 ga watan Oktoba.

Isra'ila ta kashe fiye da Falasɗinawa 46,700 inda mafi yawancinsu fararen hula ne da suka haɗa da mata da yara, kamar yadda alƙaluman ma'aikatar lafiya ta Gaza ta bayyana.

21 ga watan Nuwamba: Ƙasar Amurka da Qatar da Masar sun shirya wata ƙwarya-ƙwaryar yarjejeniyar tsagaita wuta ta mako ɗaya da ta janyo sakin waɗanda Hamas ta yi garkuwa da su 105, inda ita kuma Isra'ila ta saki wasu fursunoni Falasɗnawa 240. Isra'ila da Hamas sun ɗora wa junan su laifi kan rugujewar yarejejeniyar.

28 ga watan Disamba: Masu shiga tsakani sun soma tattaunawa kan sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta da musayar waɗanda ake riƙe da su.

2024

31 ga watan Mayu: Shugaban Amurka Joe Biden ya fitar da shawarwarin Isra'ila kan matakai uku na tsagaita wutar domin bayar da damar musayar ƴan Isra'ila da ake riƙe da su. Wannan shi ne tushen yarjejeniyar da aka amince da ita bayan watanni takwas.

10 ga watan Yuni: Kwamitin tsaro na majalisar ɗinkin duniya ya amince da ƙudirin da ke goyon bayan shirin tsagaita wutar.

31 ga watan Yuli: An dakatar da tattaunawa bayan Isra'ila ta kashe shugaban harkokin siyasa na ƙungiyar Hamas, kuma babban mai sasantawa Isma'il Haniyeh a Tehran, babban birnin Iran. An kuma cigaba da tattaunawar bayan makonni biyu, da farko ba tare da Hamas ba.

17 ga watan Oktoba: Dakarun Isra'ila sun kashe jagoran Hamas Yahya Sinwar a kudancin Gaza. Netanyahu ya kira hakan ''matakin farko na kawo ƙarshen'' yaƙin.

9 ga watan Nuwamba: Bayan shafe watanni babu wata nasara, Qatar ta dakatar da ayyukanta na shiga tsakani a tattaunawar zaman lafiyan. Ta ce dole ne Isra'ila da Hamas su sassauta buƙatun da suka gabatar. Ɓangarorin biyu sun ɗora alhakin kan junansu na rashin cigaban da ake samu.

20 ga watan Nuwamba: Amurka ta hau kujeran-na-ƙi kan ƙudirin da kwamitin majalisar ɗinkin duniya ya yi na kiran a tsagaita wuta cikin gaggawa, a cewar ta kwamitin ya yi 'watsi da' buƙatar da ake da ita ta samar da ''alaƙa tsakanin tsagaita wutar da musayar waɗanda ake riƙe da su.''

27 ga watan Nuwamba: Isra'ila ta amince da tsagaita wuta da Lebanon domin kawo ƙarshen rikicin watanni 13 da ƙungiyar Hezbollah, ƙawar ƙungiyar Hamas, wanda yaƙin Gaza ya haddasa. Hakan ya ɗaga fatan da ake da shi kan samar da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, wanda Biden ya ce zai haɗa hannu da shugabannin yankin.

2 ga watan Disamba: Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump ya ce za a fuskanci sakamako mai muni idan har ba a saki waɗanda ake cigaba da riƙe da su a Gaza ba har zuwa lokacin da zai karɓi mulki a ranar 20 ga watan Janairun 2025.

17 ga watan Disamba: Wani babban jami'i a Falasɗinawa ya ce tattaunawar bayan fage ta kai ''matakin ƙarshe'', a yayin da ministan tsaron Isra'ila, Isreal Katz ya ce an kai mataki na kusa na cimma yarjejeniyar da ba'a taɓa kaiwa ba.

2025

13 ga watan Janairu: Biden da Netanyahu sun yi magana ta waya kan tattaunawar zaman lafiyan a cikin makonsa na ƙarshe kan mulki bayan sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce ''saura ƙiris'' a cimma yarjejeniyar kuma ya na fatan kaiwa ga yin hakan kafin Trump ya ƙarbi mulki.

15 ga watan Janairu: Firaministan Qatar ya ce Israila da Hamas sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta da musayar waɗanda ake riƙe da su, kuma za ta fara aiki ne daga ranar 19 ga watan Janairu.

Biden ya ce yarjejeniyar za ta ''dakatar da yaƙin Gaza, taimaka wajen kai tallafin jin-ƙai da ake matuƙar buƙata ga fararen hula Falasɗinawa da kuma sake haɗa mutanen da ake riƙe da su da iyalansu''.