Yaya Amurka za ta kasance idan babu ƴan cirani?

Baƙi ne kashi 70 cikin 100 na masu aikin gona a Amurka, in ji nazarin hukumar kula da ayyukan ƙwadago a Amurka

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Baƙi ne kashi 70 cikin 100 na masu aikin gona a Amurka, in ji nazarin hukumar kula da ayyukan ƙwadago a Amurka
    • Marubuci, By Luis Barrucho
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 7

Cirani babbar matsala ce a zaɓen shugaban ƙasar Amurka da ke tafe, inda ƴan takarar jam'iyyun Republican da Democrat suke magana kan buƙatar a samar da tsauraran dokoki na taƙaita masu shiga ƙasar, musamman a iyakar ƙasar da Mexico.

Donald Trump ya sha yin gargaɗi kan tuɗaɗar baƙi inda kuma ya yi alƙawarin tisa ƙeyar mutane da dama da suka shiga ƙasar ta ɓarauniyar hanya ƙasashensu na asali.

Abokiyar karawarsa a zaɓen, Kamala Harris ta zargi tsohon shugaban ƙasar da ƙara ta'azzara batun ƴan cirani, amma duk da haka ta jaddada goyon bayanta ga ƙudirin samar da tsaro a kan iyakokin ƙasar da zai ƙunshi amfani da miliyoyin daloli wajen gina katanga a kan iyaka.

Sai dai wace rawa baƙi za su taka a Amurka - ƙasar da ke da yawan ƴan cirani a duniya - kuma me zai faru idan babu su a ƙasar?

Yawan al'umma

Mutane da dama sun tsallaka Amurka daga Mexico a ƙarshen 2023 amma adadin ya ragu cikin shekara huɗu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mutane da dama sun tsallaka Amurka daga Mexico a ƙarshen 2023 amma adadin ya ragu cikin shekara huɗu

Idan babu baƙi, yawan mutanen Amurka zai ragu sosai.

Yawan al'ummar Amurka ya kai miliyan 47.8 a 2023 - kashi 14.3 cikin 100 na al'ummar Amurka. Mexico ce kan gaba da miliyan 10.6 sai Indiya mai miliyan 2.8 sai China mai miliyan 2.5.

Amma yayin da adadin baƙi ya kai yawan da ba a taɓa gani ba, bunƙasar al'umma a Amurka na raguwa saboda raguwar haihuwa.

Tsakanin 2010 da 2020, ƙasar ta fuskanci raguwa sosai a yawan al'ummar ƙasar tun shekarun 1930 da yawan mutanen da ake haifa ya ragu.

Hakan na nufin Amurka, kamar sauran ƙasashe, na fuskantar ƙalubale na yawan tsofaffi inda ake samun tsadar kiwon lafiya da kuma raguwar mutanen da ke aiki.

Ana tsammanin ganin sauyi a 2040, lokacin da yawan mace-mace zai zarce yawan mutanen da ake haifa, a cewar hasashen ofishin tsara kasafin kuɗi.

Wasu masu tattalin arziki da ƙungiyoyin da ke goyon bayan baƙi sun ce ya kamata a bar baƙi su shiga ƙasar domin biyan buƙatun tattalin arzikin ƙasar musamman a yankunan karkara.

Tasirin tattalin arziki

An nuna muhawarar farko da aka fafata tsakanin Kamala Harris da Donald Trump a sansanin baƙi na Juventud da ke Tijuana a Mexico

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An nuna muhawarar farko da aka fafata tsakanin Kamala Harris da Donald Trump a sansanin baƙi na Juventud da ke Tijuana a Mexico
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wani Farfesan tattalin arziki a Jami'ar Boston, Tarek Hassan ya ce rashin baƙi zai yi tasiri a tattalin arzikin Amurka: "Idan ka cire baƙi baki ɗaya, muna magana ne kan raguwar arzikin da ake samarwa a ƙasar da kusan kashi 10 cikin 100, ma'ana arzikin kowane mutum zai ragu sannan jumullar arzikin da ake samarwa a ƙasar zai ragu sosai saboda ƙarancin mutane."

Hassan ya ƙara da cewa binciken ya nuna cewa ƴan ci-rani "na ƙara ƙirƙira da ke bunƙasa ayyuka a matakai daban-daban, don haka bai taƙaita ga wani ɓangare ba - yana ƙara ƙarfin ƙirƙira a tattalin arzikin Amurka baki ɗaya".

Akwai yiwuwar ƴan ci-ranin su kasance masu aiki. Yayin da suka wakilci kusan kashi 14 cikin 100 na al'ummar Amurka, su ne kusan kashi 19 cikin 100 na ma'aikata - miliyan 31 na ma'aikata - sannan sun fi ƴan asalin ƙasar a yawan ma'aikata, in ji ƙididdigar hukumomi.

A cewar hasashen ofishin da ke tsarawa majalisa kasafin kuɗi, kusan kashi 91 cikin 100 na baƙi ƴan shekara 16 da sama da haka da ke isa Amurka tsakanin 2022 da 2034 ana sa ran su kasance ƴan ƙasa da shekara 55, idan aka kwatanta da kashi 62 cikin 100 na al'ummar da suka kasance manya.

Wasu ɓangarorin tattalin arzikin, kamar noma, su dogara ne kan baƙi.

A cewar nazarin ma'aikatan da ke ɓangaren noma da hukumar kula da harkokin ƙwadago ta Amurka ta gudanar ya nuna kashi 70 na manoma baƙi ne sai dai galibinsu ba su da takardar izinin zama a ƙasar.

Rasa su zai jefa waɗanda suka mallaki gonaki cikin ƙalubale na neman ma'aikatan da za su shuka iri, su kuma girbe amfanin gona su kuma gyara su domin amfanin Amurkawa", in ji Nan Wu, daraktan bincike a ƙungiyar kula da ƴan ci-rani ta Amurka.

Abin da masu sukar ƴan ci-rani suke cewa shi ne kwararar baƙi ma'aikata da suke a shirye su yi aiki a biya su abin da ba a rasa ba, yana rage albashin ƴan asalin ƙasar.

Sai dai a wani bincike na 2014 da jami'ar California, Davis ta yi kan wasu bincike 27 kan tasirin baƙi a kan tattalin arziki ya yanke cewa babu wani tasiri da baƙi ke yi kan albashin ƴan asalin ƙasar.

Wani binciken baya-bayan nan da jami'ar Eastern Illinois ta gudanar ya gano cewa ƙaruwar baƙi na iya yin kyakkyawan tasirin da bai taka kara ya karya ba kan tattalin arziki.

Haraji

Baƙin da suka shiga Amurka ta ɓarauniyar hanya sun kai kashi 23 cikin 100 na baki ɗaya al'ummar ƙasar - miliyan 11 ke nan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Baƙin da suka shiga Amurka ta ɓarauniyar hanya sun kai kashi 23 cikin 100 na baki ɗaya al'ummar ƙasar - miliyan 11 ke nan

Amma mene ne tasirin haka kan haraji?

Baƙi na biyan kusan kashi ɗaya bisa shida na duk haraji - kusan dala biliyan 580 - a 2022, a cewar nazarin da AIC ya yi.

Ba wai kawai ƴan ci-ranin da suka shiga ƙasar bisa ƙa'ida bane suke biyan haraji, in ji Ms Wu daga ƙungiyar.

Ƴan ci-ranin da ke shiga ƙasar ta ɓarauniyar hanya sune kusan kashi 23 cikin 100 na duka baƙi - mutane miliyan 11, da kusan miliyan huɗu daga Mexico - a cewar nazarin da cibiyar bincike ta Pew ta yi.

Sannan wani bincike da cibiyar kula da manufofin haraji da tattalin arziki ya gano cewa ƴan ci-ranin da suka shiga ƙasar ba tare da takardu ba sun biya kusan dala biliyan 100 na haraji a matakin tarayya, da jihohi da ƙananan hukumomi a 2022.

Sai dai Daniel Costa, darakta a cibiyar ya ce duk da cewa akwai alfanun da ake samu daga ƴan ci-rani kan tattalin arziki, a wasu jihohin, ba haka lamarin yake ba, musamman a gajeren zango.

A binciken baya-bayan nan, shi da tawagarsa sun bayar da misalin kwararar baƙi da ke da albashin da bai taka kara ya karya ba amma suke iya cin gajiyar wasu tsare-tsare.

Farfesa Giovanni Peri, wani ƙwararre kan batun baƙi kuma masanin tattalin arziki daga jami'ar California, ya ce matsin lamba kan al'umomi daga baƙi na iya kamanceceniya da abin da ke faruwa idan yawan mutanen da aka haifa a Amurka ya ƙaru.

Ƙirƙira da kasuwanci

Steve Jobs, mahaifinsa ya shiga Amurka a mtsayin baƙo daga Syria, ya kafa ɗaya daga cikin manyan kamfanoni a Amurka wato Apple

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Steve Jobs, mahaifinsa ya shiga Amurka a mtsayin baƙo daga Syria, ya kafa ɗaya daga cikin manyan kamfanoni a Amurka wato Apple

Wani kaso na baƙi ko ƴaƴansu sun zama manyan ƴan kasuwa.

Kusan kashi 45 cikin 100 na mutanen da ke mujallar Fortune 500 - jadawalin kamfanoni 500 mafiya girma a Amurka ta fuskar kudin shigarsu - baƙi ne suka kafa su sannan baƙi sun gano kashi 55 cikin 100 na ƙananan sana'oi da darajarsu ta kai dala biliyan ɗaya ko fiye da haka.

Baƙi sun taka rawa sosai wajen bunƙasa ɓangaren fasaha, inda galibinsu suka shiga Amurka a matsayin ɗalibai.

A zangon karatu na 2022 zuwa 2023, fiye da baƙi ɗalibai miliyan ne suka ba da gudunmawar dala biliyan 40 ga tattalin arzikin Amurka tare da tallafa wa sama da mutum 368,000 ayyukan yi ta hanyar samar da kuɗin makaranta da na tafiyar da rayuwa, a cewar ƙungiyar malamai baƙi.

Ƙuri'ar jin ra'ayi

Wata ƙuri'ar jin ra'ayi ta baya-bayan nan ta gano cewa fiye da rabin Amurkawa na son a rage yawan baƙi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata ƙuri'ar jin ra'ayi ta baya-bayan nan ta gano cewa fiye da rabin Amurkawa na son a rage yawan baƙi

Duk da rawar da baƙi ke takawa a tattalin arzikin Amurka, wata ƙuri'ar jin ra'ayi ta gano kashi 55 cikin 100 na Amurkawa na son a rage yawan baƙi. Sannan akwai inda ra'ayi ya zo ɗaya cewa a taƙaita shigowar baƙi musamman idan aka zo ga batun tsallaka iyakar Mexico ba bisaƙa'ida ba.

Farfesa Peri ya ce wasu ƴan siyasa da ƴan jarida na kallon batun ci-rani daidai da rikici a kan iyaka, inda suke mayar da hankali kan labarai da suka shafi ɓarauniyar hanya, a maimakon tasirin ci-rani.

"Mutane suna yawan jin ci-rani a matsayin kwarara daga iyaka ta kudanci, a don haka suna tunanin yana da illa," in ji shi, a maimakon tattauna rawar da ƴan c-rani ke takawa a kan tattalin arziki da kuma ja wo raguwar mutane.

Sannan a cewar Tarek Hassan na jami'ar Boston: "Cikin shekara shirin da ta gabata, batun ci-rani ya ƙaru abin da zai iya kawo cikas ga damar karɓar ƙarin baƙi.

"Sannan yayin da ƴan ci-rani ke tasiri a tattalin arziki, da harkokin rayuwa da al'adu, ana iya samun wasu abubuwa da mutane ba su gamsu da su ba."