Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An bai wa Van Persie aikin kociyan Feyenoord
An naɗa tsohon ɗan wasan Arsenal da Manchester United, Robin van Persie sabon kociyan Feyenoord.
Mai shekara 41, wanda ya yi ritaya a 2019, ya bar horar da Heerenveen ya koma ƙungiyar da ya buga wa tamaula sau 122 da cin ƙwallo 46.
Haka kuma Van Piesie ya yi mataimakin Dick Advocaat a Feyenoord, ya kuma horar da matasan Feyenoord daga nan ya karɓi aikin kocin, Heerenveen a Mayun 2024.
Sai dai tsohon ɗan wasan tawagar Netherlands ya bar ƙungiyar tana mataki na tara a teburin Eradivisie, bayan nasara bakwai daga karawa 23.
Van Persie ya saka hannu kan yarjejeniya zuwa 2027, yayin da Rene Hake zai yi masa mataimaki, wanda ya yi aiki tare da Erik ten Hag a Manchester United.
Feyenoord tana ta uku a kan teburi da maki 11, biye da Ajax.
Ta kori kocinta, Dane Brian a makon jiya, sakamakon cin wasa ɗaya daga karawa shida a babbar gasar tamaula ta Netherlands.
Priske ya maye gurbin Arne Slot kan fara kakar bana, wanda ya koma horar da Liverpool mai buga Premier League.
Van Persie ya yi kaka takwas a Arsenal a matakin ɗan wasa tun daga 2004, wanda ya lashe FA Cup daga nan ya koma Manchester United a 2012, inda ya ɗauki Premier League a kakarsa ta farko a ƙungiyar.