Mene ne burin Isra'ila a Gabas ta Tsakiya?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Alaa Ragaie
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Arabic
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu na yawan ambaton 'Gabas ta Tsakiya sabuwa'.
Sai dai samar da daidaito a mulki da siyasar yankin ba shi ba ne a gaban Isra'ila, kuma a ƙasar akwai waɗanda suka yi amannar cewa "yanzu ne lokaci mafi dacewa" domin samun abubuwan da take so.
Taswirar da Isra'ila take so mai cike da ruɗani
Jami'an Isra'ila suna yawan fitowa da taswirar Isra'ila a tarukan duniya, sannan a bayyane yake cewa dukansu babu wanda yake saka ƴantacciyar ƙasar Falasɗinu a cikin lissafinsu.
A bayaninsa na kwana-kwanan nan a taron Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD), Netanyahu ya bayyana taswirori biyu, ɗaya a ciki akwai yankuna masu ɗaukeda koren fenti - mai ɗauke da ƙasashe da suke da yarjejeniyar zaman lafiya da Isra'ila ko kuma suke tattaunawa da su, ciki har da Masar da Sudan da UAE da Saudiyya da Bahrain da Jordan.
Na biyu kuma mai baƙin fenti, waɗanda Netanyahu ya kira da "tsinannu", kuma ya ƙara da cewa su ne Iran da ƙawayenta a yankin; Syria da Iraƙi da Yemen da Lebanon.
A wani jawabi da Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi, ya yi gargaɗi a kan abin da ya kira da "yunƙurin Isra'ila na ɓatanci."
Yezid Sayigh, wani babban masani a cibiyar Carnegie Middle East Center, ya ce "sabuwar Gabas ta Tsakiya da Netanyahu ke nema wani yunƙuri ne kawai Isra'ila take yi na yi wa Falasɗinu mulkin mallaka".
Isra'ila ba ta ɓoye burinta na faɗaɗa ƙasarta, musamman ta gefen yamma da Kogin Jordan, sannan ta sha fitowa ta bayyana burinta na gina wasu garuruwa a yankin, duk da kushe matakin da Larabawa da ƙasashen duniya suke yi.
Shi kuma David Schenker, wanda masani ne a cibiyar nazarin siyasar gabashi ta Washingoton Institute for Near East Policy ya ce: "Abin da Isra'ila take so shi ne ya zama ba ta fuskantar wata barazana daga Iran."

Asalin hoton, Getty Images
Gabas ta Tsakiya 'ba tare da bazanar Iran ba'
Da yake magana da BBC, wani masanin tsaro, Miri Eisen, wanda tsohon jami'in leƙen asirin Isra'ila ne, ya ce "ba burin Isra'ila ba ne ta tilasta wa mutane yadda take so a Gabas ta Tsakiya, tana so ne ta tabbatar da cewa Iran ba ta samu damar yin yadda take so ba".
Harin Isra'ila da ya kashe shugaban Hezbollah Hassan Nasrallah a tsakiyar birnin Beirut ma na cikin abubuwan da suka sauya akalar yaƙin da ake ciki.
Iran ta harba makamai masu linzami zuwa Isra'ila ta hanyar amfani da makaman da suka jawo hankalin ƙasashen Yamma bayan an kashe shugaban ɓangaren siyasa na Hamas, Ismail Haniyeh a ƙasarta, sannan ita kuma Isra'ila ta ce za ta mayar da martani a lokacin da ta ga ya dace.

Asalin hoton, EPA
Ƙarfin soji ba zai kawo maslaha ba
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Amurka tana ba wa Isra'ila gudunmuwa domin tabbatar da tana ci gaba da samun fifiko a yankin.
Amma a cikin sharaɗin gudunmuwar akwai cewa Isra'ila ba za ta wuce iyaka ba, kamar yadda fadar shugaban ƙasar Amurka ta sha faɗa, da kai hari a sansanin sarrafa nukiliya na Iran.
Eisen ya ce: "Aikin sojin Isra'ila na so ya hana Iran faɗaɗa aƙidunta, da kai makamai zuwa ƙungiyoyin da take ɗaukar nauyi, da sauran ƙasashe da suke mata barazana."
A cewar David Schenker: "Wataƙila Isra'ila ta ɗan samu nasarar karya lagon 'ƙungiyoyin da Iran ke ɗaukar nauyi a yankin, amma ba za ta iya fitar da sabon tsari a yankin ba, dole sai ta samu goyon bayan ƙasashen Larabawa."
Eisen ya ce Isra'ila na da burin ƙarfafa haɗakar tsaro da tattalin arziki da kimiyya da fasaha da ƙawayenta da suke da fahimta iri ɗaya a kan "barazanar Iran."
Tuni Isra'ilar ta shiga yarjejeniyar Abraham Accord da Moroko da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) da Bahrain cikin shekara huɗu.
Isra'ila ta daɗe tana son samun masalaha da Saudiyya, wadda ita kuma take so a rage ƙarfin Iran, wadda mafi yawanta ƴan Shi'a ne. Amma Saudiyya ta bayyana wa jaridar Financial Times cewa ba za ta shiga alaƙar diflomasiyya da Isra'ila ba har sai an tabbatar da ƴancin ƙasar Falasɗinu.
Kafin 7 ga Oktoban 2023, siyasa da tattalin arzikin yankin sun taka muhimmayiwar rawa wajen sauya tunanin wasu ƙasashen Larabawa irin su Masar da Syria da Lebanon da Jordan, waɗanda a baya suka ƙi amincewa da Isra'ila saboda tausayin Falasɗinwa.
"Babu shakka ƙasashen sun kasance masu tausayin mutanen Falasɗinu, sai daga baya suka gane cewa ba Isra'ilar ba ce kaɗai matsalar, har da su ma shugabannin Falasɗinu ɗin a matsalar," in ji Schenker.

Asalin hoton, Reuters
Haɗakar haɓaka tattalin arziki
Yarjejeniyar da aka riƙa shiga kafin harin 7 ga Oktoban 2023 sun ƙunshi zuba jari a harkar tsaro da tsaron intanet da makamashi da haɓaka tattalin arziki ta intanet.
Amma tun yaƙin da aka fara bayan 7 ga Oktoban 2023, sai aka fara samun tsaiko a zuba jarin tsakanin Isra'ila da sababbin abokan hulɗarta na ƙasashen Larabawa, amma duk da hakan, ƙididdiga daga Isra'ila ta nuna cewa kasuwanci tsakanin Isra'ila da ƙasashen Labarabawa biyar ya ƙaru.
Jaridar Maariv ta Isra'ila ta bayyana cewa an shiga yarjejeniya tsakanin Isra'ila da UAE, inda suka tsara wata hulɗar kasuwancin da za ta ratsa ta Saudiyya da Jordan, ta bi ta Masar. Sannan Isra'ila na samar da gas zuwa Masar.







