Van Dijk na tattaunawa da Liverpool kan tsawaita ƙwantiraginsa

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ƙyaftin ɗin Liverpool, Virgil van Dijk ya ce ya fara tattaunawa da mahukuntan ƙungiyar kan batun tsawaita yarjejeniyarsa a Anfield.

Mai shekara 33 yana tare da Liverpool tun daga Janairun 2018, wanda ƙwantiraginsa zai kare a Anfield a karshen kakar nan.

Haka shima ɗan wasan tawagar Ingila, Trent Alexander-Arnold da na Masar, Mohamed Salah yarjejeniyarsu za ta kare a karshen kakar nan.

Liverpool ta sayo Van Dijk kan £75m daga Southampton, wanda ya bayar da gudunmuwar da aka lashe Premier League da Champions League da FA Cup da League Cup da kuma Fifa Club World Cup.

A karkashin sabon koci, Arna Slot daga Netherlands a bana ya kai Liverpool matakin farko a kan teburin Premier League da cin wasa bakwai daga takwas da ya ja ragama.

Slot ya mage gurbin Jurgen Kloop, wanda ya ajiye aikin a karshe kakar da ta wuce, bayan kaka tara da ya yi a Anfield.

Ranar Laraba 23 ga watan Oktoba, Liverpool za ta kara da RB Leipzig a Champions League a Jamus, wasa na uku da za ta kara a bana a gasar zakarun Turai.

Daga nan za ta je gidan Arsenal, domin fafatawa a Premier League ranar Lahadi 27 ga watan Oktoba a Emirates.

Wasa biyu da ke gaban Liverpool:

Champions League Laraba 23 ga watan Oktoban 2024

  • RB Leipzig da Liverpool

Premier League Lahadi 27 ga watan Oktoban 2024

  • Arsenal da Liverpool