Tottenham ta kwashi rabonta a kan Man United a Premier

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Manchester United ta yi rashin nasara 3-0 a hannun Tottenham a wasan mako na shida a Premier League ranar Lahadi a Old Trafford.

Minti uku da take wasa aka fara cin United ta hannun Brennan Johnson, ƙwallo da aka zura a ragar United a kankanin lokaci a Premier tun bayan Agustan 2023 a wasa da Nottingham Forest.

Wannan shi ne karo na biyu da Tottenham ta fara cin United da wuri tun bayan Satumbar 2012 a dakika 113.

Daf da za a je hutu ne aka bai wa ƙyaftin ɗin United, Bruno Fernandes jan kati, kuma a karon farko a wasa 242 a ƙungiyar.

Jerin ƙyaftin ɗin United da aka bai wa jan kati a wasan Premier League:

  • Roy Keane a wasa da Manchester City a Afirilun 2001
  • Nemanja Vidic da Liverpool a Maris 2014
  • Wayne Rooney da West Ham a Satumbar 2014
  • Bruno Fernandes da Tottenham a Satumbar 2024

Bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne Tottenham ta kara na biyu ta Dejan Kulusevski, sai Dominic Solanke ya zura na uku a wasan.

Solanke ya ci United karo na uku a jere da ya fuskanci United ya zama ɗan Ingila da ya yi wannan bajintar bayan Jermain Defoe a Nuwambar 2002 da kuma Bukayo Saka a Janairun 2023.

Wasan da suka kara a 2023/24

Premier League ranar Lahadi 14 ga watan Janairun 2024

  • Man Utd 2 - 2 Tottenham

Premier League ranar Asabar 19 ga watan Agustan 2023

  • Tottenham 2 - 0 Man Utd

Da wannan sakamakon United ta yi rashin nasara da aka zura mata ƙwallo uku ko fiye da haka tun bayan da SirAlex Ferguson ya yi ritaya.

An zura ƙwallo uku ko fiye da haaka a United karo na 23 a fafatawa 424, idan ka kwatanta da 22 a karawa 1,035 karkashin Ferguson.