Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Napoli da Roma na zawarcin Mainoo, Tottenham na son Toney
Napoli ta tuntuɓi Manchester United tana neman ɗaukar aron ɗanwasan tsakiyar Ingila mai shekara 20, Kobbie Mainoo, a watan Janairu. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Mainoo ya kuma ɗauki hankali wata ƙungiyar ta Serie A, Roma wadda itama ke shirin ɗaukar shi a watan Janairu. (Football Italia)
Ɗanwasan tsakiyar Italiya da Newcastle Sandro Tonali na son komawa gida, AC Milan, yayin da itama Juventus ta nuna sha'awar sayen ɗanwasan mai shekara 25. (Corriere della Sera - in Italian)
Ɗanwasan tsakiyar Ingila da Aston Villa mai shekara 23, Morgan Rogers na shirin sanya hannu kan sabuwar kwangila da za ta ɗaga albashinsa zuwa fiye da £100,000 a kowanne mako. (Mail)
Bayern Munich na tattaunawa da Liverpool da kuma ɗanwasan bayan Faransa, Ibrahima Konate, kan cinikin ɗanwasan mai shekara 26. (Bild - via Get German Football News)
Liverpool da Chelsea za su shiga zawarcin ɗanwasan bayan Newcastle mai shekara 25,Sven Botman. (Caught Offside)
Tottenham na shirin sayen ɗanwasan gaban Ingila mai shekara 29, Ivan Toney, a watan Janairu daga Al-Ahli kuma kocin Spurs, Thomas Frank ya fara tattaunawa da shi. (Teamtalk)
Alexis Mac Allister ba ya da sha'awar barin Liverpool duk da tayin da ɗanwasan na Argentina mai shekara 26 ya samu daga Real Madrid. (Football Insider)
Tsohon kocin Wolves Gary O'Neil na kan gaba a jerin masu damar zama kocin Southampton. (Telegraph - subscription required)
Ɗanwasan bayan Italiya Alessandro Bastoni na son ci gaba da zama a Inter Milan, duk da ƙoƙarin Manchester United da Manchester City da kuma Liverpool na sayen ɗanwasan mai shekara 26.(Fichajes - in Spanish)