Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Van Nistelrooy bai da tabbaci ko zai ci gaba da horar da Leicester
Ruud van Nistelrooy ya ce har yanzu yana jiran ya ji ko zai ci gaba da horar da Leicester City, bayan da ta faɗi daga gasar Premier League a bana.
Leicester, wadda ta yi rashin nasara 1-0 a King Power a hannun Liverpool a makon jiya, ta tabbata cewar za ta koma buga Championship a baɗi.
Kuma ta samu maki takwas daga wasa 20 da tsohon ɗan wasan Manchester United ya ja ragamar ƙungiyar.
Van Nistelrooy, mai shekara 48, ya ce ''ya zauna da masu ƙungiyar, ya sanar da su hanyoyin da ya kamata a ɗauka, domin Leicester ta samu ci gaba.
''Na san hanyoyin da zan bi domin mayar da ƙungiyar gasar Premier League, amma sai na san matsayi na tukun na.''
Leicester City za ta fafata da Wolverhampton a Molineux ranar Asabar a gasar Premier League.
A watan Nuwamba, Van Nistelrooy ya saka hannu kan kwantiragin kaka uku a Leicester City, bayan da ta kori Steve Cooper, wanda ya yi kwana 157 a kan ragama.
To sai dai tsohon ɗan wasan United ya kasa taka rawar da ya kamata a ƙungiyar, wadda za ta koma buga Championship karo na biyu a kaka uku.
Rashin nasara da Leicester ta yi a hannun Liverpool, shi ne na 16 a gasar a wasa 18 baya - kuma karo na tara a jere da ta yi wasa a gida ba tare da cin ƙwallo ba.