Yadda aka yi cacar baki a majalisar dattijan Najeriya kan rikicin Sanata Natasha

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

A zaman jin bahasi kan sabon ƙorafin da aka shigar kan zargin neman yin lalata wanda Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan ke yi wa shugaban majalisar dattijan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio a ranar Talata, an samu zazzafan cacar baki tsakanin bangarorin biyu.

An samu sa-in-sa ne tsakanin tsohuwar ministar ilimi ta Najeriya Oby Ezekwesili da sanata mai wakiltar Ebonyi ta arewa kuma mataimakin mai tsawatarwa na majalisar, Sanata Onyekachi Nwaebonyi a lokacin da kwamitin ladabtarwa da sauraron ƙorafin jama'a na majalisar dattijai ke sauraron ƙarar ƙarkashin jagorancin Sanata Neda Imasuen.

Ezekwesili ta halarci zaman ne tare da tawagar da ke ɓangaren Sanata Natasha da suka haɗa da lauyanta Abiola Akiode da mai gabatar da ƙarar Zubairu Yakubu, yayin da Sanata Nwaebonyi kuwa na ɓangaren shugaban majalisar Sanata Akpabio a matsayin mai bayar da shaida.

Cacar bakin ta kaure ne a lokacin da mai gabatar da karar Zubairu Yakubu ya yi ƙokarin yin jawabi ga kwamitin a lokacin da Sanata Neda Imasuen ke jawabi, inda aka buƙace shi da ya kashe abun yin maganarsa, wanda ya kai ga tsohowar ministar ta sako baki.

A wata hira da ta yi da kafar talibijin ta Arise, Oby Ezekwesili ta ce tun da farko ɓangarenta sun ce ba za su yi magana ba, ko su gabatar da cikakken ƙorafin, saboda a cewar su akwai ƙararraki biyu da ke gaban kotu a yanzu.

Daga bisani a cewar ta Sanatan ya ce su ba wasa suka zo yi ba, kuma idan ba su shirya bayar da shaida ba, shi a shirye yake ya bayar da nashi.

Tsohuwar ministar ta ce bayan ya faɗi hakan ne sai ta ce mishi ya yi shiru ganin cewa su ma ba a bar su su yi magana ba, bai kamata shi ma ya yi ba, wanda kuma hakan ne ya tunzura shi ya fara jefo mata manyan kalamai na cin mutunci.

Daga nan sa-in-sar ta soma inda sanata Nwaebonyi ya mayar da zafafan kalamai kamar su 'ke wace ce da zaki ce in yi shiru?', 'ke abar kunya ce ga mata' ,'ki yi shiru da bakinki, bakinki mai wari' ', inda ita kuma ta mayar da martani cewa 'kai abin kunya ne ga majalisar dattijai'.

Sai dai duk kokarin da aka yi na sa su yi shiru ta hanyar kashe abin maganarsu, ya ci tura saboda sun ci gaba da kunnawa suna furta wa juna zafafan kalamai.

A wata hira da kafar talibijin ta Arise, Sanata Nwaebonyi ya ce ba ta mutunta shi ba a matsayin sa na Sanata, kuma a tsarin doka ya fi ta matsayi, shi ya sa ya mayar mata da kalamai dai dai da yadda ta yi masa.

Ya kuma ce shi ba da ita yake magana ba don haka bai ga dalilin da za ta sako baki ba, inda a cewar sa, in ma yayi magana ba dai dai ba, shugaban kwamitin ne ya kamata ya tsawatar masa.

Sai dai kuma ya ce yayi nadamar kalaman da yayi amfani da su a kanta saboda ta na da shekarun da za ta iya kasancewa mahaifiyarsa.

An dai dage zaman sauraron sabon karar da Sanata Natasha ta shigar har sai bayan kotu ta yanke hukunci kan wasu kararraki biyu da ke gabanta.