Har da ni a matsalar da ta hana Man United cin wasa - Ten Hag

Asalin hoton, Reuters
Kocin Manchester United Erik ten Hag ya ce har da shi cikin waɗanda ya kamata a zarga saboda rashin taɓuka abin kirki a wasa da FC Twente na Europa League ranar Laraba.
Christian Eriksen ne ya fara ci wa United ƙwallo a minti na 36 a cikin yadi na 18, kafin daga baya Sam Lammers ya farke ta bayan dawowa daga hutun rabin lokaci kuma wasa ya tashi 1-1.
Shi ne wasa na farko da United ta buga a gasar ta zakarun Turai da aka sauya wa fasali, kuma hakan na nufin ƙungiyar wasa ɗaya kacal ta ci cikin tara da ta buga a wasannin zakarun Turai da suka gabata.
Da yake magana bayan tashi daga wasan, ɗanwasan tsakiya Eriksen ya ce rawar da suka taka a wasan "ba ta isa ba".
Shi ma mai horarwa Ten Hag ya amince da abin da Eriksen ya faɗa yana mai cewa tabbas Twente sun fi su ƙoƙari kuma har da shi kansa a cikin matsalar.
"Sun buga wasan iya ƙarfinsu," in ji Ten Hag. "Sun karaɗe ko'ina da ina amma mu ba haka abin yake ba. Kashi 99 cikin 100 ba mu yi ƙoƙari ba.
"A lokuta da dama nakan ji cewa tunanin tawagarmu yana da kyau. Amma a yau [Laraba], ina da magana. Ba wai 'yanwasa ne kawai za su sauya hali ba, ni ma ina ciki. Ba haka ya kamata mu yi ba.
"Kun san muna da matsalar jefa ƙwallo a raga, amma ya kamata a ce mun ci wasan nan."
United za ta ziyarci FC Porto a wasanta na gaba a gasar ranar 3 ga watan Oktoba, daga baya kuma ta je gidan Fenerbahçe SK a Turkiyya, wadda tsohon kocinta Jose Mourinho ke jagoranta.












