'Chelsea ba za ta taɓuka abin kirki ba sai ta rage ƴan wasa'

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Kocin Chelsea Enzo Maresca ya ce za a iya samun 'matsaloli' idan kulob ɗin bai iya rage yawan manyan ƴan wasansa ba kafin a rufe kasuwar saye da sayar da ƴan wasa.

Blues ta ɗauko ƴan wasa 11 a wannan bazarar wanda ya sa adadin manyan ƴan wasan ƙungiyar ya kai sama da 40.

A farkon makon nan, Maresca ya ce ƴan wasan Ingila Raheem Sterling da Ben Chilwell na cikin rukunin ƴan wasa kusan 15 da aka ce su yi atisaye da tawagar matasan ƙungiyar.

'Babu wani koci a duniya da zai iya aiki tare da ƴan wasa 45. Ba abu ne mai yiwuwa ba, ba za a iya yin hakan ba.' In ji Maresca

An cire Sterling daga cikin ƴan wasan farko na gasar Premier ta Maresca, a wasan da Manchester City ta doke su da ci 2-0 ranar Lahadi, yayin da kuma bai buga wasan farko na gasar cin kofin Europa da suka yi da Servette ranar Alhamis.

Da alama dai wasu ƴan wasa da dama ba su da tabbas kan makomarsu a ƙungiyar, ciki har da masu tsaron baya Ben Chilwell da Axel Disasi da Trevoh Chalobah, da kuma ɗan wasan tsakiya Carney Chukwuemeka.