Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ya sa nake so gwamnatin Najeriya ta daina biyan tallafin man fetur - Ɗangote
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta daina biyan tallafin man fetur domin a cewarsa "tallafin mai zai janyo kashe kuɗaɗen gwamnati da bai kamata ba".
Ɗangote wanda ya bayyana hakan a wata hira da tashar Bloomberg ranar Litinin, ya ce gwamnatin shugaba Tinubu ba za ta iya ci gaba da biyan tallafin man ba.
"Ina ga lokaci ya yi da Najeriya za ta janye tallafin mai baki ɗaya domin dukkannin ƙasashe sun daina biyan shi.
Farashin manmu (Najeriya) kusan kaso 60 na farashjin mai a maƙwabtan ƙasashe kuma iyakokinmu na da girma saboda haka ci gaba da biyan zai yi wuya. Gwamnati ba za ta iya ci gaba da biyan tallafin ba."
Dangote ya ƙara da cewa man fetur ɗin da matatarsa ke fitarwa zai taimaka wajen farfaɗo da darajar naira.
"Batun tallafin fetur magana ce babba. Idan ka bayar da tallafi a kan wani abu, wasu sai su riƙa ƙara yawan abun domin su samu ƙarin kuɗaɗe sannan sai nauyin ya ƙare a kan gwamnati. Zai fi dacewa a daina biya baki ɗaya." In ji Ɗangote.
Dangane da yadda matatarsa za ta taimaka, Ɗangote ya ce:
"Matatarmu za ta magance matsaloli da dama. Za ta bayyana asalin adadin man fetur da ake amfani da shi a Najeriya saboda babu wanda zai iya faɗa maka a yanzu adadin litar man fetur da ake amfani da shi. Wasu za su ce maka lita miliyan 60 a kullum, wasu suna cewa bai kai ba. Amma mu yanzu za mu iya ƙididdigewa. Sannan za mu saka na'urorin bibiyar motocinmu domin tabbatar da cewa a Najeriya suke sauke man."
'Wahalhalun da na sha kafin kafa matatar mai'
Ɗangote ya ce bai taɓa tunanin zai fuskanci irin wahalar da ya fuskanta ba kafin cimma kafa matatar mansa.
Mun shekara biyar kafin mu cimma kudurinmu "mun ƙaddamar da aikin gina matatar a 2013, inda muka samu matsaloli da gwamnatin jiha inda muka sayi filin gina matatar a wata jiha da ke maƙwabtaka da jihar Legas, inda suka yi ta yin wasa da hankalinmu har kusan shekaru uku da rabi abin da ya tilasta mana barin can zuwa Legas. Mun je Legas inda can ma muka samu matsaloli da al'ummun can. Al'amarin dai ya ɗauke mu kusan shekara biyar kafin mu fara.
Duk wannan ya faru ne bayan mun ɗauki bashin dala biliyan 2.4 domin fara aikin kuma kuɗin ruwa a kan bashin kullum hauhawa yake. Amma dai da haka muka ci gaba." In ji Ɗangote.
Attajirin mai kuɗi na biyu a Afirka ya ci gaba da cewa "bayan nan kuma akwai batun gina tashar ruwa da sauransu. Daga nan ne kawai muka yanke shawarar mu zama kamfanin da yake kwangilar ginin da sayen kayan aikin da kuma harkar injiniya.