Mazaɓu 16 da za a yi zaɓen cike gurbi a ranar Asabar a Najeriya

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Hukumar Zaɓen Najeriya, INEC, ta ce ta kammala dukkannin shirye-shiryen da suka kamata gabanin gudanar da zaɓukan cike gurbi a mazaɓu 16 a faɗin Najeriya ranar Asabar.

Zaɓen ya ƙara samun tagomashi ne kasancewar ya zo a daidai lokacin da siyasar ƙasar take ƙara ɗaukar zafi, tun bayan da jam'iyyun adawa a ƙasar suka fara yunƙurin dunƙulewa wuri ɗaya domin fuskantar babbar jam'iyyar ƙasar mai mulki a babban zaɓen ƙasar.

Wannan ya sa wasu suke ganin tamkar wannan zaɓen dama ce ta nuna ƙwanji tsakanin haɗakar ta jam'iyyun adawa a gefe guda da kuma jam'iyyar mai mulki, inda ake ganin wataƙila zaɓen zai iya zama wata ƴar manuniya game da akalar siyasar ƙasar.

ADC za ta gwada ƙarfinta

Tuni dai tsohon ɗantakarar shugaban ƙasa a jam'iyyar Labour, Peter Obi ya buƙaci magoya bayansa su zaɓi ADC a zaɓukan.

Haka ma sauran jagororin hamayyar da suke da zaɓe a jihohinsu, kamar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, wanda aka hango a saman mota yana tallafa ƴantakararsa domin su samu ƙuri'a.

Ita dai hukumar zaɓen ƙasar ta ce ta shirya tsaf domin gudanar da zaɓen, inda ta yi kira da a fito gudanar da zaɓe cikin lumana.

Mazaɓu 16 a jihohi 12

A wata sanarwa da INEC ta fitar game da zaɓen wanda za a yi a gobe Asabar, ta ce ƴantakara za su fafata ne domin maye gurbin kujeru 16 daban-daban a jihohin ƙasar guda 12.

Sanatoci biyu

  • Mazaɓar Anambra ta Kudu
  • Mazaɓar Edo ta Tsakiya

Majalisar wakilai biyar

  • Edo
  • Jigawa
  • Kaduna
  • Ogun
  • Oyo

Majalisar jiha tara

  • Adamawa
  • Anambra
  • Kaduna
  • Kogi
  • Neja
  • Taraba
  • Zamfara.
  • Kano - kujeru biyu

Kujerar sanatan Edo ta Tsakiya, ita ce wadda gwamnan jihar na yanzu, Sanata Monday Okpebholo ya ajiye domin shiga takarar gwamnan jihar, inda ya samu nasara a zaɓen.

Haka kuma mataimakinsa Denis Idahosa, tsohon ɗanmajalisa ne mai wakiltar mazaɓar Ovia North/Ovia a majalisar wakilai, wanda hakan ya sa nan ma za a yi zaɓen cike gurbi.

A Anambra kuma, sanatan Anambra ta Kudu, Sanata Ifeanyi Ubah ya rasu ne a bara, wanda hakan ya sa za a maye gurbin da ya bari.

INEC ta ce yaƙin zaɓe zai ƙare kamar yadda dokar ƙasar ta tanada, sannan ta yi kira ga ƴanƙasar da ƴantakara da jam'iyyunsu da masu sa ido da su yi amfani da doka da oda, wanda ta ce hakan zai sa ta gudanar da zaɓen cikin sauƙi, kamar yadda kwamishinan hukumar mai kula da yaɗa labarai da ilimantar da masu ƙada zaɓe, Sam Olumekun mni ya fitar.