Manchester United za ta kara korar ma'aikata 200

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United za ta kara rage ma'aikata 200, ''domin ƙungiyar ta koma samun ribar kasuwanci.''
An kori ma'aikata kimanin 250 a bara a shirin da shugaba, Sir Jim Ratcliffe ya ɗauka na rage kashe-kashen kuɗin ƙungiyar, domin samun riba.
A wani taro da ma'aikata ranar Litinin, babban jami'i Omar Berrada ya sanar da ma'aikata cewar za a sake rage mutane a wani sabon tsari, domin bunkasa United.
A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ''Wannan shirin ana yi ne domin mayar da ƙungiyar kan yadda za ta ke cin riba, bayan hasara a kaka biyar a jere tun daga 2019.
Ta kara da cewar ''Tana ɗaukar wadan nan matakan, domin bunkasa United da samar da kuɗin shiga ta yadda za a haɓɓaka ingantattun ayyukanta.''
''"Wannan zai samar da ingantaccen tsarin kudi, inda ƙungiyar za ta iya saka hannun jari a kwallon kafa ta maza da mata da kuma ingantattun ababen more rayuwa."
Berrada ya ce: "Muna da alhakin sanya Manchester United a matsayi mafi girma don samun nasara a cikin kungiyoyinmu na maza da na mata da kuma makarantar horar da matasa.''.
"Wadannan hukuncin mai tsauri ya zama dole mu ɗauka, don mayar da ƙungiyar kan ingantaccen tsarin hada-hadar kudi.
''Muna hasarar ƙudi a shekara biyar baya a jere, ba za mu bari hakan ya yi ta faruwa ba.
"Babban abubuwan da muka sa a gaba a matsayin kungiya shine samar da nasara a filin wasa ga magoya bayanmu da kuma inganta kayan aikin mu. Ba za mu iya saka hannun jari kan wadannan manufofin ba idan har muna ci gaba da asarar kudi."










