Mahari ya hallaka ƙananan yara huɗu da jikkata wasu a Brazil

Motoci a inda aka kai harin

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Maharin ya haura katangar makarantar yaran ne da gatari
An wallafa

Akalla kananan yara hudu ne wani mutum da ke dauke da gatari ya hallaka a wata makarantar renon yara da ke birnin Blumenau a kudancin kasar Brazil, kamar yadda jami’ai suka sanar.

Akwai kuma wasu yaran hudu da mutumin mai shekara 25, wanda ya haura makarantar ya raunata ranar Laraba.

Daya daga cikin yaran na cikin mawuyacin hali kamar yadda rahotanni suka bayyana.

‘Yan sanda sun gaya wa ‘yan jarida cewa maharin ya mika kansa, inda yanzu yake tsare a hannunsu.

Jami’an kwana-kwana sun ce mutumin ya kashe yara maza uku da yarinya daya a filin wasan da ke cikin makarantar.

Ana ganin shekarun yaran sun kama daga tsakanin hudu zuwa bakwai.

Akwai kananan yara kusan arba’in a cikin makarantar (Cantinho Bom Pastor nursery), a lokacin da aka kai harin.

Jami’an sun kara bayani da cewa mutumin ya haura katangar makarantar ne wadda ba ta gwamnati ba ce, inda ya rika kai wa yaran harin kan mai-uwa-da-wabi.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wata malama a makarantar Simone Aparecida Camargo, ta bayyana lamarin da cewa abu ne da ba za ka taba tunanin ganinsa ba a rayuwa.

‘’Wata abokiyar aikinmu ta bazamo da gudu tana cewa ‘rufe kofa, rufe taga, wani mutum ya shigo makarantar. Da farko mun dauka fashi da makami ne saboda ya yi kokarin ya karya kofar ya shigo, saboda haka na kulle yaran a ban-daki, daga nan sai wata ta zo tana cewa mutumin ya shigo ya yi kisa ne.’’

Malamar ta ce dukkanin yaran suna filin wasa a lokacin harin.

Ms Camargo ta kara da cewa bayan gatarin mutumin yana dauke da wasu makaman ko da yake ba ta fayyace wadanne iri ne ba.

Jin labarin ke da wuya sai iyaye cikin firgici suka rika garzayawa zuwa makarantar domin duba ‘ya’yansu.

Hukumomin birnin na Blumenau sun dakatar da aiki a makarantar zuwa akalla washegari.

Gwamnan jihar Santa Catarina inda birbin yake ya ayyana kwana uku na zaman makoki.

Wannan ba shi ne karon farko da aka taba kai hari makarantar renon yara a jihar ba.

A 2021 wani matashi mai shekara 18 ya taba kai hari kan wata makarantar ta renon yara inda ya kashe malamai biyu da kananan yara uku a babban birnin jihar.

Lamarin ya faru bayan kwana 10 kacal da wani matashion dan shekara goma sha ya kashe wata malama ta hanyar daba mata wuka, ya kuma raunnatu wasu hudu a wata makaranta a São Paulo.

Shugaba Luiz Inácio Lula da Silva ya nuna alhininsa a wani sakon Twitter da ya rubuta, yana cewa, ‘’ ba ciwon da ya kai a ce iyali sun rasa ‘ya’yansu ko jikokinsu musamman ma kuma a ce ta hanyar ta’addanci ne a kan kananan yaran da bas u ji b aba su kuma gani ba, wadanda ba za su iya kare kansu ba.’’

Birnin da abin ya faru yana da mazauna kusan dubu 360, kuma sanannen gari ne da ‘yan yawan bude idanu ke yawan zuwa saboda kayan tarihi na Jamusawa da ke yankin.