Ku San Malamanku tare da Malam Saminu Ɗorayi
Filin Ku San Malamanku na wannan makon ya karɓi baƙuncin Malam Saminu Ibrahim Ɗorayi, wanda shi ne babban limamin masallacin Ɗorayi Babba a Jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya.
An haifi malamin a garin Kano a shekarar 1940 - yana da shekara 82.
Malamin ya ce bai yi maraicin karatu ba saboda yawan almajiran mahaifinsa, inda limamin Ɗan-Bare Malam Halilu da limamin Ɗorayi Malam Sani suka fi yin fice.
Ya ƙara da cewa a hannunsu ne ya yi karatu mai yawa bayan ya sauke Al-Ƙur'ani mai tsarki a hannun mahaifinsa.
"Na ji ciwo da ɓacin rai lokacin da na ga ana kallon malaman-soro a matsayin ba komai ba - ba ka da wani abu idan ba karatun shaida ka yi ba," a cewar shehin malamin.
"Wannan dalilin ya sa na ce 'bari mu yi karatun nan na takarda, ko dai ba mu samu boko ba ma samu shahada [shaidar karatu]'.
"Sai na shiga SAS (kwalejin harshen Larabci). Bayan na gama kuma na shiga Jami'ar Bayero, inda a nan na yi difiloma da digiri."



