Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Pakistan na neman agajin ƙasashen duniya kan mummunar ambaliya
Ƙasar Pakistan na kira ga ƙasashen duniya da su kai mata ɗauki sakamakon ambaliyar da ta yi wa ƙasar illa.
Tuni dai Amurka da Birtaniya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa suka bayar da da tallafinsu.
Sai dai akwai buƙatar ƙarin tallafi mai yawa, kamar yadda wani ma'aikacin ofishin harkokin cikin gida na ƙasar ya shaida wa BBC.
Tun da farko dai Firaiministan Pakistan din ya bayyana cewa bala'in da ake ciki a ƙasar ya wuce tunanin jama'a, bayan mummunar ambaliyar ruwan da ta yi sanadin mutuwar kusan mutu dubu ɗaya.
Shehbaz Sharif ya bayyana haka a lardin Sindh inda yankin na daga cikin wuraren da ambaliyar ta shafa.
An yi ƙiyasin cewa an zabga ruwa kusan ninki takwas kan yadda ake samun ruwan sama a watan Agusta a lardin.
Bayan kusan mutum dubu da suka rasu, akwai dubban mutane da suka rasa muhallansu, miliyoyi kuma lamarin ya shafe su ta wani fannin.
Ambaliyar ruwa ba sabon abu ba ne a Pakistan, sai dai mazauna ƙauyukan da lamarin ya shafa sun ce ba su taɓa ganin bala'i a rayuwarsu makamancin wannan ba.
Kusa da birnin Larkana, akwai dubban gidajen ƙasa da ruwa ya shanye.
Abin da za a iya hangowa daga nesa kawai shi ne saman itatuwa.
Wuraren da kuma ruwan bai shanye sosai ba, ana hangen rufin gidajen mutane waɗanda ruwa ya shanye.
Akwai wani ƙauye da al'ummarsa ke cikin tsananin buƙatar abinci, kamar yadda bayanai suka nuna.
A wani kauyen kuma, akwai yara da yawa waɗanda suka kamu da cutuka da ake samu sakamakon gurɓataccen ruwa.
A lokacin da wata babbar motar ɗaukar kaya ta shiga wani ƙauye, sai jama'a da dama suka bi motar da gudu.
Wata yarinya mai shekara 12 ta bayyana cewa ita da ƴar uwarta sun shafe kwana daya ba su ci komai ba.
"Ba mu samu abinci ba, kuma akwai ƴar uwata da ba ta da lafiya, tana ta amai tuntuni," kamar yadda yarinyar ta bayyana.
A ɗaya daga cikin manyan titunan birnin Sukkur, akwai ɗaruruwan mutane waɗanda tuni suka yada zango a can.
Da dama daga cikinsu sun fito ne daga ƙananan ƙauyuka kuma sun samu labarin cewa an fi samun taimako a cikin birni.
Ko a ranar Juma'a sai da Firaiministan ƙasar ya bayyana cewa wannan ambaliyar ta shafi mutum miliyan 33, kusan kashi 15 cikin 100 na jama'ar ƙasar.