Shin sau nawa aka kara tsakanin Real da Chelsea ne?

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Ranar Juma'a aka raba jadawalin Champions League karawar quarter finals, inda aka hada wasa tsakanin Real Madrid da Chelsea.

Real ta kawo wannan matakin, bayan da ta fitar da Liverpool da cin 6-2 gida da waje a kakar bana.

Ita kuwa Chelsea ta yi nasarar yin waje da Borussia Dortmund da cin 2-1 gida da waje.

Sau hudu suka kara a Champions League, amma sau bakwai suka hadu a gasar zakarun Turai jimilla.

Kungiyar da Graham Potter ke jan ragama, wadda ta kai daf da na kusa da na karshe bayan cin Dortmund ta kuma kara da Inter Milan da Dynamo Zagreb a cikin rukuni.

Raheem Sterling ya ci wa Chelsea kwallo uku a Champions League a bana.

Real Madrid wadda ta ja ragamar rukuni na shida da maki 13 ta fafata da RB Leipzig da Shakhtar Donetsk da kuma Celtic Glasgow.

Vinicius Junior na Real Madrid ya zura kwallo shida a raga a Champions League na bana, shine kan gaba a kungiyar a kakar nan.

Real Madrid ce za ta fara karbar bakuncin Chelsea a Santiago Bernabeu a wasan farko ranar 11 ga watan Afirilu.

Sannan Chelsea ta karbi bakuncin wasa na biyu a Stamford Bridge ranar 19 ga watan Afirilu.

Chelsea tana da Champions League biyu, ita kuwa Real ita ce mai rike da na bara kuma na 14 jimilla.

Wasa tsakanin Real Madrid da Chelsea

2021/2022 Champions League

  • Real Madrid 2 - 3 Chelsea
  • Chelsea 1 - 3 Real Madrid

2020/2021 Champions League

  • Chelsea 2 - 0 Real Madrid
  • Real Madrid 1 - 1 Chelsea

1998/1999 European Super Cup

  • Chelsea 1 - 0 Real Madrid

1970/1971 Euro Cup Winners Cup

  • Chelsea 2 - 1 Real Madrid
  • Chelsea 1 - 1 Real Madrid