Waiwaye: Alkawarin hukunta makisan sojoji da kuɓutar da mutum 16 da aka sace a Kaduna

An wallafa

Wannan makala ce da ke duba muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi.

Dole ne a hukunta waɗanɗa suka kashe mana sojoji 17 - Tinubu

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ce waɗanda suka kashe sojoji a jihar Delta za su fuskanci hukunci, yana mai gargaɗin cewa gwamnatinsa ba za ta amince da kai hare-hare kan sojoji da ababen more rayuwa ba.

Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin shugabannin majalisar dattawan kasar a yayin wani zaman cin abincin buɗe baki a fadar gwamnati a ranar Alhamis.

Tinubu ya ce sojoji za su ci gaba da samun goyon bayan gwamnatinsa wajen kawar da barazanar tsaro a faɗin kasar.

"Rundunar sojojinmu na aiki tukuru, kuma ba za mu bar maharan su lalata mutunci da ƙimar sojojinmu da kuma shugabancinta ba."

Ɗalibai biyu sun mutu a turmutsutsun karɓar tallafi a Nasarawa

Akalla ɗalibai mata biyu na jami'an jihar Nassarawa da ke Keffi ne suka mutu sakamakon wani turmutsutsu da aka yi a wajen karbar kayan tallafi na gwamnati a dandalin taro na jami'ar da safiyar Juma'a.

Gwamnatin jihar Nasarawa dai ta yi amfani da dandalin taron da ke jami'ar ne wajen raba kayan tallafin wahalar rayuwa ga ɗaliban jami'ar.

Wani ɗan jarida da ya shaida yadda al'amarin ya faru ya shaida wa BBC cewa ɗaliban mata da suka rasu na daga cikin waɗanda suka je neman tallafin.

Mataimakain gwamnan jihar ta Nasarawa, Emmanuel Akadeh wanda ya je jami'ar domin jajantawa dangane da faruwar al'amarin ya ce faruwar al'amarin na da takaici kuma "za mu kafa kwamitin da zai binciko hakikanin abin da ya faru.

Shaguna '180' sun ƙone a gobarar babbar kasuwar Sokoto

Wata gobara da ta tashi a babbar kasuwar jihar Sokoto a safiyar Litinin ta yi sanadin ƙonewar shaguna da dama a ɓangaren masu sayar da babura da kekuna.

Garba Muhammad Gwazi, shugaban ƴan mashin reshen jihar ya shaida wa BBC cewa gobarar ta laƙume shaguna '180' na masu sayar da mashin.

A cewarsa, har yanzu ba a san abin da ya janyo tashin gobarar ba da ta janyo asarar dukiya ta miliyoyin naira. Sai dai ya ce gobarar ta soma ne daga wata shara da aka tara.

Ya bayyana cewa gobarar ba ta kai ga asarar rai ko jikkata ba.

Gwazi ya kuma yi kira ga gwamnati ta kai masu ɗauki domin "kasuwancinmu ya miƙe ya ci gaba." in ji shi.

Sojoji sun kuɓutar da mutum 16 da ƴanbindiga suka sace a Kajuru

Sojojin Najeriya ƙarƙashin runduna ta ɗaya sun kuɓutar da mutum 16 da ƴanbindiga suka sace a yankin Kajuru da ke jihar Kaduna.

Sun kuma daƙile yunƙurin wata ƙungiyar miyagu na yin garkuwa da mutane.

Cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na rundunar sojin, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya fitar, rundunar ta ce sojojin da aka tura ƙarƙashin runduna ta ɗaya sun daƙile yunƙurin sace mutane tare da ceto mutanen da aka sace a yankin Tantatu da ke ƙaramar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.

A cewar sanarwar, sojojin sun kai samamen ne bayan bayanan sirrin da suka samu ranar Lahadi da daddare lokacin da suka bi sawun ƴanbindigar da suka sace wasu mutane a ƙauyen.

"Sojojin na ci gaba da gudanar da bincike a cikin dazuka domin ganowa tare da tseratar da sauran mutanen da aka yi garkuwa da su tare da murƙushe miyagun ayyukan ƴanbindiga," in ji sanarwar.

Kotu ta ƙi amincewa da belin Nnamdi Kanu

Mai sharia'a Binta Nyako ta Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Talata, ta ki amincewa da belin shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu.

Sai dai kotun ta bayar da umarnin a gaggauta sauraron shari’ar Kanu wanda ke fuskantar tuhume-tuhumen da suka shafi cin amanar kasa.

Kanu, wanda aka gabatar da shi gaban kotu a ranar Talata, yana tsare ne a hannun hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) tun bayan kama shi a watan Yunin 2021 domin yanke hukunci kan neman belin sa.

Nyako ta ce kotun za ta bayar da damar ci gaba da sauraron shari’ar ne kawai, sannan ta umarci masu gabatar da kara da su gabatar da shaida na farko.

Lauyan Kanu, Aloy Ejimakor, ya nuna rashin jin dadinsa da hukuncin.

Ma'aikatan jami'o'in Najeriya sun fara yajin aiki saboda hana su albashi

Ƙungiyar manyan ma’aikatan jami’o’in Najeriya (SSANU) da ƙungiyar da ba ta malamai ba (NASU) ta soma yajin aikin gama-gari a fadin kasar domin nuna rashin amincewarsu da abin da suka dauka a matsayin rashin adalci da kuma sabani na biyan albashi da gwamnatin tarayya ke yi.

Shugaban SSANU, Mohammed Ibrahim, ya tabbatar da fara yajin aikin a cikin shirin “The Morning Brief” na gidan Talabijin na Channels, inda ya bayyana cewa ma’aikata a sassan jami’o’i daban-daban sun shiga yajin aikin.

Ya kuma jaddada cewa wannan mataki zai ci gaba har tsawon kwanaki bakwai masu zuwa matukar gwamnati ba ta magance kokensu ba.

Ya bayyana rashin jin dadinsa game da rashin samun hanyar sadarwa a hukumance daga wakilan gwamnati.

Ya bayyana damuwarsa game da yiwuwar masu zagon kasa a cikin gwamnati, yana mai tambayar dalilin da ya sa wasu jami’ai ba su cika umarnin shugaban kasa Bola Tinubu na biyan alawus-alawus na 2022 ga mambobin kungiyar jami’o’i ba.