Fernandez ya je sansanin Chelsea ya kuma nemi afuwa

Enzo Fernandez

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Enzo Fernandez ya nemi afuwar 'yan wasan Faransa da waɗanda ke Chelsea, bayan da abokin wasansa, Wesley Fofana ya zarge shi da "wariyar launin fata mara ma'ana".

Ɗan wasan Argentina, mai shekaru 23, ya je Atlanta ta Amurka, ya kuma yi jawabi kan bidiyon da aka wallafa a shafinsa na sada zumunta bayan da Argentina ta doke Colombia 1-0 a wasan karshe a Copa America ranar 14 ga watan Yuli.

Bidiyon ya kunshi wata waka da wasu daga cikin 'yan wasan Argentina suka rera kan 'yan ƙwallon Faransa bakar fata, wanda hukumar kwallon ƙwallon Faransa ta ce ya ƙunshi wakokin wariyar launin fata da nuna wariya.

An gabatar da korafi ga hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa, yayin da Chelsea ta sanar cewar za ta ɗauki matakin ladabtarwa.

Chelsea tana da 'yan wasan Faransa bakwai wadanda bakar fata da suka haɗa da Axel Disasi, Benoit Badiashile, Lesley Ugochukwu, Christopher Nkunku, Malo Gusto da Fofana, duk suna cikin wwaɗanda Chelsea ta je da su Amurka.

Fofana, wanda ya buga wa Faransa wasa ɗaya, ya sanya hoton bidiyon a Instagram, yana mai bayyana shi a matsayin "wariyar launin fata da ba ta ma'ana".

BBC ta fahimci cewa 'yan wasa da dama sun yaba da tattaunawar da suka yi da sabon kocio, Enzo Maresca, wanda ya sanar da ranar da ɗan wasan Argentina zai je Amurka inda Chelsea ke buga wasannin sada zumunta.

Maresca ya yi watsi da batun lokacin da aka tambaye shi a makon da ya gabata a taron manema labarai kan matsayin kocin, sai dai ya ce bai yi tunanin za a samu "wata matsala kwata-kwata ba" idan Fernandez ya koma ƙungiyar.

Fifa tana ci gaba da gudanar da bincike, wanda watakila za a iya dakatar da Fernandez buga wasu wasannin a Chelsea.