Champions League: Bayern da PSG sun ƙetara zuwa zagayen quater-final

Asalin hoton, Rex Features
Harry Kane ya zura ƙwallaye biyu a gasar cin kofin zakarun Turai inda Bayern Munich ta farfado daga tuntuɓen da ta yi a wasan farko ta doke Lazio da ci 3-0, a wasan da aka buga a filin wasan Allianz arena.
Bayan da aka tashi 1-0 a wasan farko da aka buga a Rome, Bayern ta fara samun kwanciyar hankali a lokacin da Kane ya zura ƙwallon farko a minti na 38 da fara wasa.
Thomsa Muller ya ƙara ƙwallo na biyu a ƙarin lokaci a ƙarshen rabin lokaci na farko kafin Kane ya ƙara zura ƙwallonsa na biyu a minti na 66.
Ƙungiyar Thomas Tuchel ta kasance cikin fargabar fuskantar kakar wasa ta farko ba tare da wani babban kofi ba tun 2011-12.
Wannan nasarar ta sa Tuchel ya ci gaba da kasancewa da fatan cewa Bayern za ta lashe kofin gasar zakarun Turai karo na bakwai kafin tsohon kocin na Chelsea ya bar ƙungiyar a ƙarshen kakar wasa ta bana.
A ɗaya wasan da aka buga da daren talata, Kylian Mbappe ya taka rawar gani inda ya zura ƙwallaye biyu yayin da Paris St-Germain ta doke Real Sociedad da ci 2-1 a filin wasan San Sebastian.
Hankali duk ya karkata kan Mbappe, wanda ya amince da komawa Real Madrid a wannan bazarar.
Kuma dan wasan na Faransa ya nuna bajintarsa inda ya ci ƙwallayensa na 27 da na 28 a kakar bana.
Yanzu PSG da Bayern za su jira ƙungiyoyin da za su kara da su a zagayen daf da na kusa da na ƙarshe, bayan kammala wasannin zagayen ƴan 16 a mako mai zuwa.
A ranar Juma'a 15 ga watan Maris ne za a fitar da jadawalin zagaye na takwas na ƙarshe a gasar.









