Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Reece James ba zai buga gasar kofin duniya ba
Da kyar idan Reece James zai buga wa Ingila gasar kofin duniya, bayan da Chelsea ta sanar zai yi jinyar mako takwas.
Mai shekara 22, wanda ya yi wa tawagar Ingila wasa 15, ya ji rauni a gwiwar kafarsa a wasan da Chelsea ta ci AC Milan 2-0 a Champions League ranar Talata.
Nan da mako biyar za a fara gasar kofin duniya, wato ranar 20 ga watan Nuwamba a Qatar, wadda za ta karbi bakunci wasannin a karon farko.
Wasu masu tsaron bayan Ingila da ke jinya sun hada da Kyle Walker na Manchester City da Trent Alexander-Arnold na Liverpool.
Walker ya ji rauni ne tun farkon watan Oktoba, shi kuwa Alexander-Arnold ya ci karo da koma baya ne a wasa da Arsenal a makon jiya.
Walker ya ce yana fatan zai murmure da wuri, domin yana kwadayin buga gasar kofin duniya.
Wanda ake sa ran zai maye gurbin shi ne dan wasan Newcastle United, Kieran Trippier.
Chelsea ta tabbatar da cewar likitoci sun yi wa dan wasan aiki a makon nan.