Anya Klopp zai kai labari a Liverpool kuwa a bana?

An wallafa

Liverpool ta sha kashi a wasan farko a cikin rukuni a Champions League kakar bana, bayan da Napoli ta doke ta 4-1 a ranar Laraba.

Napoli ta fara cin kwallo a minti na biyar da fara wasa ta hannun Piotr Zielinski a bugun fenarity.

A minti na 18 Victor Osimhen ya buga fenariti amma bai ci kwallo ba, daga baya Andre Zambo Anguissa' ya ci na biyu.

Daf da za a je hutu ne Napoli ta kara na uku ta hannun Giovanni Simeone ya kara na uku, sannan Piotr Zielinski ya ci na hudu kuma na biyu a wasan.

Liverpool ta zare daya ta hannun Luis Diaz.

Kungiyar Anfield ta kai wwasan karshe a kakar da ta wuce a Champions League, inda Real Madrid ta yi nasara da ci 1-0 a Faransa.

Hakan ne ya sa kungiyar Sifaniya ta lashe kofin zakarun Turai na 14 jumulla, ba wadda ta lashe kofin da yawa kamarta.

Wasannin da Klopp ya ja ragama a kakar bana

Community Shield Asabar 30 ga watan Yuli                          

  • Liverpool             3 - 1       Man City             

Premier League Asabar 6 ga watan Agusta           

  • Fulham 2 - 2       Liverpool            

Premier League Litinin 15 ga watan Agusta          

  • Liverpool             1 - 1       Crystal Palace   

Premier League Litinin 22 ga watan Agusta          

  • Man Utd              2 - 1       Liverpool            

Premier League Asabar 27 ga watan Agusta         

  • Liverpool             9 - 0       Bournemouth  

Premier League Laraba 31 ga watan Agusta         

  • Liverpool             2 - 1       Newcastle          

Premier League Asabar 3 ga watan Satumba       

  • Everton                0 - 0       Liverpool            

Champions League Laraba 7 ga watan Satumba

  • Napoli 4 - 1 Liverpool

Ranar 10 ga watan Satumba Liverpool za ta karbi bakuncin Wolverhampton a gasar Premier League.

Daga nan ta karbi bakuncin Ajax a wwasa na biyu a Champions League a cikin rukuni ranar Talata 13 ga watan Satumba.