Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Harin Isra'ila ya hallaka Falasdinawa akalla 10
Mutane akalla goma ne suka rasu a wasu hare-hare ta sama da Isra’ila ta kai Zirin Gaza, a cikin dare, wadanda sojinta suka ce sun hari mambobin kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Islamic Jihad ne.
Hukumomin Falasdinu sun tabbatar da mutuwar mutane goma da kuma wasu da ba su tantance yawansu ba da suka samu raunuka.
A sanarwar da kungiyar Falasdinawan ta fitar ta ce wasu manyan shugabanninta Al-Quds Brigades wato reshenta na soji uku sun yi shahada a hare-haren na cikin dare.
Rundunar ta ce, daga cikin wadanda suka mutu akwai kwamandojinta uku, wadanda ta bayyana sunayensu da- Jihad Shaker Al-Ghannam da Khalil Salah Al-Bahtini Al-Bahtini da kuma Tariq Muhammad Ezzedine.
Kungiyar ta ce mutanen uku sun rasa rayukansu tare da matansu da kuma wasu daga cikin ‘ya’yansu.
Sai dai ba ta bayar da wani cikakken bayani a kan matan ko yawan ‘ya’yan ko shekarunsa ba.
A sanarwar da ta fitar kungiyar ta ce yayin da take makokin rasuwar shugabannin shahidanta tare da mata da ‘ya’yansu ta ce ko da wai mutuwarsu ba za ta sa ta karaya ba sai dai kara mata karfi da ci gaba a gwagwarmayarta da yardar Allah.
Rahotanni sun ce wadanda suka ga hare-haren sun yi bayaninin cewa sun ji fadawar makaman da suka fashe a kan rufin wani gini a Birnin Gaza da kuma wani gida a birnin Rafah da ke kudanci.
Sojin Isra’ila sun ce sun hari gidajen mambobin kungiyar gwagwarmayar ta Falasdinawa ta Islamic Jihad, uku, wadanda ta zarga da alhakin kai hare-haren roka yankunanta a baya-bayan nan.
A makon da ya gabata Isra’ila ta yi ruwan makamai a zirin na Gaza mai tarin jama’a, bayan makaman roka da aka harba mata, a matsayin martani na mutuwar wani fitaccen Bafalasdine da ke yajin cin abinci, a gidan yarin Isra’ilar, Khader Adnan.
Adnan, wanda dan gwagwarmaya ne da ke da alaka da kungiyar Islamic Jihad, ya rasu ne bayan kusan wata uku na yajin cin abinci.
Ya kaurace wa abincin ne tsawan kwana 87 domin kin yarda da tsare shi ba tare da tuhuma ba in ji wata kungiya ya Falasdinawa fursunoni.
Ruwan bama-baman na Israila na makon da ya gabata, ya lalata wurare da dama a Zirin na Gaza, tare da hallaka jama’a da raunata wasu.
Daga baya dai kura ta lafa bayan da jami’an Qatar da Masar da kuma na Majalisar Dinkin Duniya sun shiga tsakani aka samu tsagaita wuta.
A bisa tsammanin martanin Falasdinawa ta hanyar harba rokoki, a kan hare-haren da Isra’ilar ta kai a daren da ya gabata, sojin Isra’ilar sun shawarci jama’a da ke zaune a yankuna kasar da ke tazarar kilomita 40 daga Gaza su tabbatar sun kasance kusa wuraren da aka samar na musamman na kariya daga hare-haren bam.