Ku San Malamanku tare da Abu Qatada Arabi

Bayanan bidiyo, Ku San Malamanku tare da Abu Qatada Arabi
Ku San Malamanku tare da Abu Qatada Arabi
An wallafa

Shirin Ku San Malamanku na wannan makon ya tattauna tare da Abu Qatada Muhammad Arabi.

Abu Qatada na ɗaya daga cikin limaman Masallacin Usman Bn Affan da ke unguwar Gadon Kaya a Kano, Najeriya.

Malamin haifaffen ƙaramar Unguwar Makafin Dala ne a jihar Kano. A can ya fara wayo har suka koma Unguwar Rijijyar Lemo.

Ya fara ne da karatun allo inda daga baya ya koma islamiyya.

Bayan sun koma Unguwar Gadon Kaya ya ci gaba da karance-karancensa na Al-kur'ani da sauran littattafan addini.

Ku kalli bidiyon don ganin cikakkiyar hirar.