Kane ya ci kwallo uku rigis ya zura 12 a Bundesliga

An wallafa

Kyaftin ɗin Ingila, Harry Kane ya ci ƙwallo mai ƙayatarwa daga yankin gidansu da cin uku rigis a wasan da Bayern Munich ta casa Darmstadt 8-0.

Kane wanda ke taka rawar gani a Bundesliga tun bayan da ya koma Jamus da taka leda a bana ya zura 12 jimilla a gasar.

Bayan da suka koma zagaye na biyu Kane ya fara cin ƙwallo a wasan da aka yi jan kati uku, daya daga Bayern da biyu daga Darmstadt.

Leroy Sane da Jamal Musiala da kuma Thomas Muller kowanne ya zura kwallo a raga a karawar.

Daga nan ne Kane ya samu ƙwallo daga gidansu ya kuma buga ta ta yi tsiri ta wuce golan darmstadt ta fara raga.

A karawar ce mai tsaron ragar Bayern Munich, Manuel Neuer ya koma wasa a karon farko, bayan da ya karya ƙafa lokacin yana zamiyar kankara a Disambar 2022.

Da wannan sakamakon Bayern tana jan ragamar teburin Bundesliga da tazarar maki daya, amma za a iya ɓaro da ita da zarar Bayer Leverkusen ta ci Freiburg ranar Lahadi.

Kungiyar da Thomas Tuchel ke jan ragama za ta fuskanci Borussia Dortmund a makon gaba.

Ita kuwa Darmstadt tana mataki na 14 da tazarar maki biyu tsakaninta da 'yan gurbin ƙarshe.